Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Motar Ɗalibai Wuta, Sun Tafka Mummunar Ɓarna
- Wasu mutane ɗauke da bindigu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari kan motar ɗaliban makaranta a jihar Enugu
- An tattaro cewa maharan sun kashe ɗaliba mace ɗaya yayin da wasu da dama su ke kwance rai hannun Allah a Asibiti
- Shugaban makarantar ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai harin ne bayan sun tashi daga makaranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Wasu ƴan bindiga da ake zaton Fulani ne sun farmaki motar ƴan makaranta mallakin kwalejin St Paul da ke Eke, ƙaramar hukumar Udi a jihar Enugu.
Ƴan bindigan, waɗanda ake zargin su ke yawan yin garkuwa da mutane a yankin, sun kashe ɗaliba ɗaya mace yayin da wasu da dama suka ji raunuka daban-daban.
Jaridar The Nation ta samu labarin cewa da yawa daga cikin wadanda suka samu raunukan harbin bindiga a halin yanzu suna kwance rai hannun Allah a wani asibiti da ba a bayyana ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda maharan suka farmaki Motar Bas ta ɗalibai
An tattaro cewa yan bindigan sun bude wa motar Bas din ɗaliban wuta da nufin tilasta wa diraban ya tsaya, amma diraban ya yi ta maza ya ƙi tsayawa.
A wani faifan bidiyo da ke yawo, an ga gawar ɗalibar da maharan suka kashe da kuma sauran ɗaliban da suka tsira daga harin.
Wata murya a bidiyon ta bayyana cewa:
"Makiyaya sun kai wa dalibanmu hari a hanyar komawa gida bayan tashi daga makaranta, an harbe daya daga cikinsu har lahira, wasu hudu kuma sun ji raunin harbi."
“Duba gawar karamar dalibar da suka kashe, wannan na cikin mawuyacin hali, (ya nuna wata da ke kwance) muna addu'ar Allah ya sa ta rayu, sau huɗu suka harbe ta."
Shugaban makarantar, Rebaran Fada Frank a wata hira ta wayar tarho da manema labarai, ya tabbatar da harin, kamar yadda The Sun ta ruwaito.
"Eh da gaske ne, mun tashi makaranta da misalin ƙarfe 3:30 jiya, a hanyar komawa gida ne aka kai wa ɗaliban hari, da yawa sun samu raunuka, daga baya ɗaya ta mutu," in ji shi.
Duk wani yunƙuri na jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe, ya ci tura.
Yan banga da Fulani sun yi artabu a Neja
A wani rahoton kuma Mutum biyu sun mutu yayin da ƴan banga da Fulani suka yi arangama a kasuwar Beji, ƙaramar hukumar Bosso a jihar Neja.
Rahoto ya nuna cewa mutum bakwai na kwance a Asibitin Beji ana kula da lafiyarsu bayan samun rauni a faɗan da ya auku.
Asali: Legit.ng