Mutane Sun Mutu Yayin da Fulani Suka Yi Arangama da Ƴan Banga a Kasuwar Jihar Neja

Mutane Sun Mutu Yayin da Fulani Suka Yi Arangama da Ƴan Banga a Kasuwar Jihar Neja

  • Mutum biyu sun mutu yayin da ƴan banga da Fulani suka yi arangama a kasuwar Beji, ƙaramar hukumar Bosso a jihar Neja
  • Rahoto ya nuna cewa mutum bakwai na kwance a Asibitin Beji ana kula da lafiyarsu bayan samun rauni a faɗan da ya auku
  • Kwamishinan harkokin makiyaya da kiyo na jihar Neja ya gargaɗi kowane ɓangare su guji ɗaukar doka a hannunsu

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum biyu yayin da wasu Bakwai ke kwance a asibitin Beji ana musu magani biyo bayan wani artabu da aka yi a jihar Neja.

An yi arangama tsakanin fulani da yan banga a Neja.
Mutane Sun Mutu Yayin da Yan Banga Suka Yi Artabu da Fulani a Kasuwar Jihar Neja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wannan lamari ya faru ne sakamakon wata musayar wuta da aka yi tsakanin Fulani da ƴan banga a kasuwar mako-mako da ke ci a garin Beji, ƙaramar hukumar Bosso, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun buɗe wa motar ɗalibai wuta, sun tafka mummunar ɓarna

Garin Beji, wanda yanki ne na noma yana da kasuwar dabbobi da hatsi kuma garin na da nisan kilomita 30 daga Minna, babban birnin jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban asibitin Beji, Aliyu Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Daily Trust yayin da ya kai masu ziyara ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa an kawo mutane tara da faɗan Fulani da ƴan bangan ya shafa zuwa Asibitin ɗauke da raunuka iri daban-daban.

Ya ce mutum biyu daga cikin sun riga mu gidan gaskiya yayin da ragowar mutane 7, dukkansu ƴan Fulani suna kwance ana ci gaba da ƙoƙarin yi musu magani.

Wane mataki Gwamnatin jihar zata ɗauka?

Kwamishinan makiyaya da harkokin kiyo na jihar Neja, Umar Rabe Sands, ya tabbatar da aukuwar lamaɗin inda ya yi gargaɗi mai zafi kan ramuwar gayya.

Ya ce gwamnatin Neja zata zauna da masu ruwa da tsaki na kowane ɓangare domin lalubo hanyoyin warware rikicin Fulani da manoman Gbagyi, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Bom ya halaka manyan kwamandojin CJTF 2 da wasu mutum 4 a Borno

Ya kuma gargadi bangarorin biyu da su daina daukar doka a hannunsu, yana mai cewa akwai hanyoyi daban-daban na warware takaddama ba tare da tayar da hankali ba.

Zamfara ta sa matsalar tsaro a gaba

A wani rahoton na daban Dauda Lawal ya yi kira ga hukumomin tsaro su ƙara danƙon hadin kai a tsakanin su domin tabbatar da tsaro a Zamfara.

Gwamnan ya bayyana cewa tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma ne babban abin da ya sa gaba a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262