Bom Ya Halaka Kwamandojin CJTF 2 da Wasu Mutum 4 a Borno
- Wasu kwamandojin ƴan sakai na CJTF da ke yaƙi da ƴan Boko Haram sun rasa rayukansu a wani harin bam
- Kwamandojin biyu da wasu mutum huɗu sun rasa ransu ne bayan motarsu ta taka wani abun fashewa da aka binne a ƙarƙashin ƙasa
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa dukkanin mutanen da ke cikin motar sun rasa rayukansu sakamakon taka abun fashewar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Wasu kwamandojin Civilian JTF guda biyu sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wani bom da ake kyautata zaton na ƴan ta'addan Boko Har ne a kusa da ƙauyen Ndufu da ke ƙaramar hukumar Ngala a jihar Borno.
Majiyoyin tsaro da mutanen yankin sun bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Daily Trust.
Wani babban kwamandan CJTF, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa waɗanda harin ya rutsa da su sun ci karo da bom ɗin da aka binne a bakin hanya a kan hanyarsu ta zuwa sintiri na yau da kullum a ƙauyen Ndufu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum nawa ne suka rasu a harin?
"Babban kwamandan Gambarou, Bukar Goni, da kwamandan da ke kula da yankin Ngala, Malam Cede na daga cikin mutum shida da ke cikin motar kuma duk sun rasu." A cewar majiyar.
Hakazalika an tattaro cewa tawagar ƴan sakan na CJTF sun bar garin Ngala da misalin karfe 3 na dare domin yin sintiri a yankin Ndufu, inda a ƙofar shiga garin Ndufu, motarsu ƙirar (Hilux) ta fashe a lokacin da ta taka abun fashewa inda dukkansu suka rasu.
Koƙarin yin magana da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso Kenneth, bai yi nasara ba domin bai amsa kiran waya ba, kuma bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba.
Ƴan Ta'addan Boko Haram Sun Halaka Mutane a Borno
A wani labarin kuma, mayaƙan Boko Haram sun salwantar da rayukan wasu mutum huɗu a wani hari da suka kai a jihar Borno.
An halaka mutanen ne a wani ayarin motocin da suka haɗa da ƴan sakai na CJTF da sojoji waɗanda ke raka fasinjoji a kan hanyar Gwoza-Limankara.
Asali: Legit.ng