"Ya Sa Na Yi Karyar Kurumta, Ya Cinye Kudina" - Wata Mata Ta Fallasa Fasto Mai Mu'ujizar Karya

"Ya Sa Na Yi Karyar Kurumta, Ya Cinye Kudina" - Wata Mata Ta Fallasa Fasto Mai Mu'ujizar Karya

  • Wata budurwa yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya bayan wani fasto ya ki biyanta cikon N100k da take bin shi bayan ta yi karyar kurumta a wani shirinsa na bogi
  • A wani shirin mu'ujiza na bogi, an dauko matashiyar don ta taka rawar kurma kan N200k amma N100k kawai aka biyata
  • A cewarta, abun da ta yi ba daidai bane a wajen Allah amma ta ce ta haka ne take samun na kashewa a matsayinta na yar makaranta

Wata dalibar makaranta ta kwancewa wani fasto zani a soshiyal midiya kan kin bata cikon N100k da take binsa bayan ta yi karyar kurumta a wani shirin mu'ujiza na bogi.

Wata mai amfani da Facebook, Nenye Uzowulu, ce ta fito da maganar idon duniya bayan dalibar ta aike mata da sako a dandalin.

Kara karanta wannan

Kamar wasa, wata mata ta koma yin rarrafe a taron biki, bidiyon ya girgiza intanet

Matashiya ta wankewa fasto zani a kasuwa
An yi amfani da hotunan don misali ne basu da alaka da labarin Hoto: Thomas Lohnes, Kujenga Amani
Asali: Getty Images

Sai dai kuma, ta ki bayyana sunan dalibar ko kuma na faston da ake magana a kansa.

Kamar yadda labarin dalibar ya nuna, faston ya biya ta N100k a matsayin somin tabi domin ta yi karyar kurumta a yayin wani shirin mu'ujiza, tare da alkawarin cika mata N100k a wannan rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makonni biyu bayan nan, matashiyar ta ce bata samu cikon kudinta. Ta ce hadiminsa na musamman yana ta ikirarin cewa aiki ya sha kansa a duk lokacin da ta kira shi a wayar tarho.

Ta yarda abun da ta aikata ba daidai bane

Yayin da take bayyana cewa abun da ta aikata ba daidai bane a wajen Allah, matashiyar ta bayyana cewa tana bukatar kudin don toshe bukatunta na makaranta, tana mai cewa ba za ta iya karuwanci ba. Ga cikakken rubutunta:

Kara karanta wannan

“Ina ta mugayen mafarkai”: Budurwa ta koka bayan ta farke matashin kai da ta siya N800

"Nenye ki wallafa sannan ki boye sunana saboda ina tafarfasa.
"Wani fasto ya biya ni N100k don na yi karyar kurumta wanda bayan ya yi mu'ujizar za a biyani N100k cikon kudina da yamma!
"Yanzu makonni biyu kenan ba a biyani cikon 100,000 dina ba. Duk lokacin da na kira shi a waya hadiminsa zai dauka ya ce mun aiki ya sha kansa. Na san abun da na aikata ba daidai bane a wajen Allah. Amma ni daliba ce da ke fadi tashi don daukar dawainiyar makaranta.
"Karuwanci abu daya ne da na sha alwashin ba zan taba yi ba a rayuwata. Ya dade yana amfani da kawayena kuma yana biyansu. Me yasa zai rike mun kudina. Ta yaya zan samu cikon kudin don Allah.
"Hatta mutumin da ya hada mu yana fada mani na yi hakuri. Har sai yaushe!"

Jama'a sun kadu da jin labarin

Chidinma Grace Onwuemene ta ce:

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

"Yar'uwata ki roki yafiyar Allah sannan ki ci gaba da harkokin, saboda duk wani malamin bogi da zai iya abun yaudararwa zai iya yin koma menene na mugunta, kawai ki kyale shi...A nawa ra'ayin kenan."

Ifesinachi Hope Ugochukwu ya ce:

"Ya dade da na cire hannuna daga duk abun da ya shafi fasto ko wani."

Queen J Gold ta ce:

"Ya biya mutumin da ya hada ki da shi, baaba abubuwa na faruwa."

Agogo ya hado fasto da mabiyansa

A wani labarin kuma, wani fasto daga garin Missouri dake Amurka yayi suna bayan bidiyonsa ya bayyana inda yake caccakar masu bauta kan yadda suka gaza siya masa agogon Movado mai matukar tsada.

A wa'azinsa, Fasto Carlton Funderburke na cocin Well dake Birnin Kansas, an ji a bidiyo yana sukar mambobin cocin inda yake kiransu da fatararru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng