Fasto ya hau kan ryuwan cikin wata a coci

Fasto ya hau kan ryuwan cikin wata a coci

Wani Fasto wanda ke ikirarin yana da ikon mayar da ruwa zuwa barasa, ya hanye kan ruwan cikin wata yar cocin sa.

Wani da aka fi sani da Apostle Joshua Gambe, shugaban cocin Harvest Family International Ministry a Zimbabwe, wanda ya taba ikirarin zai iya rubanya abunda Yesu Kristi yayi a littafin injila lokacin da ya mayar da ruwa zuwa barasa a gurin aure, yayi wani abu mai daure kai a taron yan cocinsa.

Fasto ya hau kan ryuwan cikin wata a coci
Fasto Joshua Gambe ya dare kan cikin wata mamba

An rahoto cewa Gambe yana zaban mambobin cocinsa kan suyi bacci tukuna kafin ya haye kan ruwan cikinsu ya tsaya, a matsayin wata hanya na nuna masu ikon sa.

Yace:

“Suna bacci kamar wanda suka mutu, kuma domin ku tabbatar da cewa a sume suke, zan haye kan ruwan cikinsu na kuma yi tsalle a kansu. Ya kai matsayin da har na kira matar da ke da nauyin kilogram 80 ta haye kansu tayi tsalle, kuma zasu kasance cikin al’ajabin gannin hotunansu kuma bazasu ji ciwo ko kadan ba a jikinsu a lokacin da na tayar dasu.

Fasto ya hau kan ryuwan cikin wata a coci
Fasto Gamble

KU KARANTA KUMA: An saki yan matan Chibok 21

Da yake Magana kan labarin daukakarsa, shugaban yace:

 “Mun fara a garajin wani gida a Kuwadzana da mutane kasa da guda koma amma ma’aikatar ta bunkasa sosai a kullun da mutane fiye da 300 a kowani Lahadi a cikin kasa da shekaru biyu.”

Da akayi hira dashi a kasar Zimbabwe, shugaba Gambe yace:

 “Ina ba ruwa umurni ya zama barasa kuma domin a tabbatar da cewan ruwan ya bi umarnin da na bashi,. Ina bayar da wani daga cikin ruwan da na komar barasa ga mutane su sha kuma sais u fara maye. An kuma ce ba wai ruwan yana canza launi bane ko dandano bane, a’a dandanonsa na nan kamar yadda yake amma da zaran mutun ya sha zai fara maye."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng