"Ina Kwance a Asibiti Na Kusa Mutuwa": Jigon APC Mara Lafiya Ya Koka
- Fitaccen ɗan gwagwarmayar nan na Najeriya, Frank Kokori ya koka kan rashin lafiyan da yake fama da shi
- Kokori wanda tsohon babban sakataren ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta ƙasa (NUPENG) ne, ya ce ya jima yana kwance a asibiti
- Kokori ya koka da yadda kungiyar NUPENG ba za ta iya kula da shi ba a wannan mawuyacin lokaci na rayuwarsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Warri, Jihar Delta - Tsohon shugaban ƙungiyar kwadago, Dr. Frank Kokori, ya ce yana fama da matsanancin rashin lafiya.
A wani kiran gaggawa da ya yi wa jaridar Nigerian Tribune da misalin karfe 12:40 na daren ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, jigon na jam'iyyar APC ya ce wata cuta mai alaƙa da ƙoda da yake fama da ita na iya kawo ƙarshen rayuwarsa.
Kokori na shan wuya a asibiti
Kokori ya tabbatar da cewa "abin kunya ne ga Najeriya" yayin da aka bar shi yana jinya a ƙaramin asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan fafutukar wanda haifaffen jihar Delta ne, ya bayyana cewa na’urar sanyaya iska (AC) ta asibitin da yake jinya, ba ta yin aiki saboda haka kwata-kwata rayuwa ba ta yi masa daɗi.
A kalamansa:
"Ku gaya wa duniya cewa Kokori ya mutu kuma ya tashi. Asibiti ɗaya tilo a Warri da zai iya magance matsalar ƙoda shi ne asibitin Horeb da ke Warri.
“Amma ina fuskantar wasu ƙalubale. Na'urar sanyaya iska ba ta aiki. Wannan wace ƙasa ce!".
"Ku tattara kanku. Ina da abin da zan gaya wa ƙasar nan, don Allah. Don Allah, ku yi iya ƙoƙarinku."
"Faɗa musu cewa zan iya biyan ko nawa ne, amma su kunna mini AC saboda ina jin jiki."
Datti Baba-Ahmed abokin takarar Obi ya bukaci Tinubu da Shettima su yi murabus, ya bayyana dalilansa
"AC ta mutu. Don Allah ku yi iya ƙoƙarinku ku kunna ta. Zan iya sake dawowa da rai amma ina son duniya ta sani cewa idan na rayu, zan kunyata shugabannin ƙasar nan."
"Sun ji kunya. Ta yaya Kokori zai kasance a ƙaramin asibiti. Jama'a suna yin iya ƙoƙarinsu don na san cewa matsalar rashin man dizal ne."
"AC ta mutu. Biyu daga cikin ƴaƴa na suna nan tare da ni. Na tura daga cikinsu zuwa wajen mahukuntan asibitin ya gaya musu cewa su yi duk mai yiwuwa su kunna AC, idan na fita zan biya saboda ina jin jiki."
Ya ƙara da cewa:
"Ina kira ga NUPENG cewa wannan shi ne abin da za su yi wa shugabanninsu ke nan."
"Akwai takaici NUPENG ta kasa kula da ni. Abun akwai baƙin ciki. Allah ya sakawa kowa da alkhairi."
Kokori na ɗaya daga cikin waɗanda suka yi gwagwarmayar ranar 12 ga watan Yunin 1993.
Ya bayar da gudunmuwa a yunƙurin nuna adawa da soke zaben shugaban kasa da aka yi ranar 12 ga watan Yuni wanda aka yi amanna cewa Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola ne ya lashe zaɓen.
APC Ta Yi Magana Kan Rashin Lafiyar Gwamnan Edo
A baya rahoto ya zo kan yadda jam'iyyar ta yi bayani kan rashin lafiyar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akinkunrin Akeredolu.
Jam'iyyar ta nuna ƙwarin gwiwar ta kan cewa nan bada daɗewa ba Gwamna Rotimi zai dawo ya ci gaba da jan ragamar jihar.
Asali: Legit.ng