Kudin Litar Man Fetur Zai Iya Saukowa Bayan Faduwar Kudin Ganga a Duniya

Kudin Litar Man Fetur Zai Iya Saukowa Bayan Faduwar Kudin Ganga a Duniya

  • Sai da gangar danyen mai ya koma kasa da fam $80 a makon nan a lokacin da duniya ta ke tunanin farashin zai harba
  • Karyewar farashin zai taimakawa ‘yan kasuwa da masu motoci da abubuwan hawa da za su rika sayen mai da araha
  • Gwamnatoci da kasashen irin Najeriya da su ka dogara da mai domin samun kudin shiga ba za su ji dadin labarin ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Farashin gangar danyen mai na Brent ya karye zuwa $80 a kasuwar duniya, hakan ya faru ne a tsakiyar makon nan da ake ciki.

Rahoton Bloomberg ya bayyana cewa wannan ne karon farko da mai ya yi irin wannan faduwa tun watan Yulin shekarar nan ta 2023.

Kara karanta wannan

An Kama Mutane 4 Kan Laifin Satar Kujerar Bandaki Na Gwal Daga Fadar Blenheim

Man fetur
Aikin hako man fetur Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A ranar Larabar nan an saida gangan Brent a kan kasa da $79.80, hakan ya nuna farashin ya sauka da 2%, sai daga baya ya koma $79.8.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Man Brent da WTI sun karye

Gidan jaridar ta ce gangar WTI kuwa ya karye zuwa $75.44 ne a kasuwannin duniya.

Craig Erlam mai nazarin kasuwa a kamfanin OANDA ya bayyana cewa a cikin watanni uku da su ka wuce, man bai taba faduwa haka ba.

An yi tunanin man fetur zai tashi

MSN ta ce masana su na ganin duk ganga za ta iya zarce $150 idan aka gagara kawo karshen yakin sojojin Israila da Dakarun Hamas a Gaza.

Abin da ya jawo canjin farashin ba zai rasa nasaba da rage amfani da fetur da dizil da aka yi ba musamman a Sin mai fuskantar kalubale ba.

Kara karanta wannan

An Damfari ‘Dan Kasuwa An Sulale da Motar N6.2m Ana Tsakiyar Gwajin Lafiyar Inji

Farashin ya na yawo ne a sakamakon labarin da ake samu cewa kayan da ake fita da su daga kasar Sin sun ragu a watan jiya na Oktoba.

Fetur zai sauko a Najeriya?

Idan gangan danyen mai ya yi araha, watakila hakan ya yi tasiri a Najeriya a daidai lokacin da ake kokawa da farashi saboda an cire tallafi.

Muddin Dala ta rage daraja kuma gangan danyen man bai tashi ba, akwai yiwuwar farashin litar fetur ta ragu a gidajen man da ke Najeriya.

Sai dai ana kishin-kishin cewa ko a yanzu da ake sayen fetur har a N660 a wasu wurare, gwamnati ta na biyan tallafin man a asirce.

Za a fara tace man fetur a gida

A baya ana da rahoto idan abubuwa sun tafi daidai, NNPCL zai rika saidawa Dangote danyen mai a farashin kasuwa, shi kuma zai tace.

Da zarar an rattaba hannu a yarjejeniyar NNPCL da Dangote, masana su na tunanin cewa za a samu saukin harkar man fetur a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng