Yan Kwadago Sun Mamaye Filin Jirgin Saman Abuja, Fasinjoji Sun Yi Cirko-Cirko, An Soke Jirage
- Kungiyoyin kwadago na gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya Abuja
- Hakan na cikin matakin da kungiyoyin NLC da TUC suka dauka don tabbatar da hana jirage fita da ko zuwa jihar Imo
- Wannan dai ya biyo bayan farmakin da aka kai wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero a jihar Imo
FCT, Abuja - Mambobin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun tattara kansu don gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja, a ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, kungiyoyin kwadagon sun taru a filin jirgin saman da misalin karfe 8:58 na safe, don tursasa umurnin da suka ba mambobinsu da ke aiki a ma'aikatar sufurin jiragen saman na hana gaba daya jiragen da za su Owerri, babban birnin jihar Imo tashi.
Yan kwadagon sun shammaci matafiya da suka isa filin jirgin saman yayin da fasinjoji suka yi cirko-cirko.
Ajaero: Masu zanga-zanga sun toshe hanyar shiga filin jirgin saman Abuja
Zanga-zangar na daga cikin matakan da kungiyoyin kwadagon biyu suka ce za su dauka kan jihar Imo bayan farmakin da aka kai wa shugaban NLC, Joe Ajaero, rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin kungiyoyin sun tattaru tare da yi wa hanyoyin shiga da fita daga filin jirgin zobe, yayin da suke zanga-zanga kamar yadda suka sanar a taron manema labarai da ya gudana a Abuja.
An hana motoci samun damar shiga cikin filin jirgin don daukar fasinjoji. Haka kuma, fasinjoji na takawa da kafa don isa bakin titi wanda ke da nisa daga filin jirgin domin samun ababen hawa yayin da wasu ke takowa ciki da kafa don kada su rasa jiragensu.
An samu cunkoson ababen hawa sosai a hanyar filin jirgin yayin da masu motoci ke jiran a kawo karshen zanga-zangar.
A halin da ake ciki, an ga matafiya suna tattauna lamarin yayin da suka daura laifin a kan gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma kan matakin da yan kwadago suka dauka bayan harin da aka kai wa Ajero.
An hana jirage fita da zuwa Imo
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa kungiyoyin kwadago a masana’antar sufurin jiragen sama sun bayar da umarnin janye ayyukansu a kan duk wani jirgi da zai tashi zuwa garin Owerri, jihar Imo, a kafatanin filayen jiragen saman Najeriya.
Wannan dai na zuwa ne a matsayin 'bin umarnin' kungiyar kwadago da ta kunshi kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC bayan cin zarafin shugaban NLC, Joe Ajaero a makon da ya gabata a Owerri.
Asali: Legit.ng