Gwamna Mai Ci Ya Sake Bankado Badakalar Makudan Kudade Har Biliyan 1 Kan Ministan Tinubu
- Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya sake bankado badakalar makudan kudade na fiye da biliyan daya
- Gwamnan na zargin tsohon Gwamna Matawalle da ware makudan kudaden kan otal da wurin cin abinci da aka barsu fiye da shekaru
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala ya fitar a jiya Laraba 8 ga watan Nuwamba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sake fitar da sabon rahoto na badakalar kudade da ake zargin minista Bello Matawalle.
Gwamnatin ta zargi Matawalle da salwantar da fiye da biliyan daya kan gyaran wani otal da wurin shakatawa, Legit ta tattaro.
Wa ya ke zargin Matawalle kan badakala?
Kakakin gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a jiya Laraba 8 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idris na kalubalantar Matawalle da ya yi bayani yadda ya fitar da kaso 93 na makudan kudade ga kamfanin Circle Construction and Engineering LTD.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin ta himmatu wurin tabbatar da gaskiya da kuma dakile badakalar makudan kudade, Premium Times ta tattaro.
Mene ake zargin Matawalle a kai?
Sanarwar ta ce:
"A kokarin tabbatar da gaskiya da dakile cin hanci gwamnatin ta yanke shawarar tono badakalar da gwamnatin Matawalle ta yi.
"Tsohon gwamna Matawalle ya barnata dukiyoyin al'ummar jihar Zamfara a lokacin mulkinsa."
Wannan na zuwa ne bayan Matawalle ya zargi Dauda Lawal da ma sa kage don raba shi da mukamin minista da Tinubu ya ba shi na karamin ministan tsaro a kasar.
Matawalle ya yi martani kan zargin da ake ma sa
A wani labarin, karamin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya yi martani game da zarge-zargen da Gwamna Dauda Lawal ke yi a kansa.
Matawalle ya bayyana cewa gwamnan na kirkirar karairayi don bata ma sa suna da kuma son raba shi da kujerarshi ta Minista.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya sha kaye a hannun Dauda Lawal a zaben da aka gudanar a watan Maris.
Asali: Legit.ng