Abin Da Ya Faru Bayan An Sace Daliban Jami'ar Zamfara – Matawalle Ya Magantu
- Tsohon gwamnan jihar Zamfara, kuma ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ba da labarin abin da ya faru bayan sace daliban jami'ar tarayya ta Gusau
- Matawalle ya ce lokacin da shugaban kasa ya ba su umurnin zuwa jihar Zamfara, sai gwamnan jihar Lawal ya bar kasar, don kulla makircinsa
- Sai dai Gwamna Lawal ya karyata wannan zargi na Matawalle, in da ya bayyana cewa ya bar Najeriya ne don halarartar taron Majalisar Dinkin Duniya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana yadda Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ki amsa kiran da ya yi masa, ana tsaka da jimamin sace daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau.
Mista Matawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar, a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta DCL Hausa, a daren jiya Litinin, ya ce Mista Lawal “ya gudu” daga jihar kwana guda bayan sace daliban a lokacin da tawagar gwamnatin tarayya ke kokarin haduwa da shi don tattauna batu kan sace daliban.
‘Yan siyasar biyu dai sun fara takun-saka ne tun farkon yakin neman zabe a shekarar 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Lawal, dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ya doke Mista Matawalle na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yayin fafatawar zaben, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Gwamna Lawal ya ki daukar kiranmu - Matawalle
Tsohon gwamnan yana magana ne akan sace dalibai 24 na jami’ar tarayya ta Gusau da 'yan ta'adda su ka yi a watan Satumba.
"Lokacin da aka sace daliban jami'ar, Lawal na Zamfara amma sai ya gudu da safe, ya tafi Amurka saboda makircinsa."
"Bayan faruwar lamarin, Shugaban kasa ya kira mu (Minitocin tsaro) tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, ya ce mu je Zamfara, mu jajanta musu, sannan mu gana da Gwamnan jihar tare da kai ziyara jami’ar."
"Amma na rantse da Allah na kira shi kuma na kira mataimakinsa, babu wanda ya amsa kiran da na yi. Zan nuna muku shaidar kiran wayar don ku gani da kanku."
Tsohon gwamnan ya ce tawagar ba ta je jihar Zamfara ba, tunda gwamnan ba ya kasar don kaucewa haifar da tunanin cewa suna siyasantar da rashin tsaro a jihar.
Gwamna Lawal ya yi martani
Da yake mayar da martani kan zargin, mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala-Idris, ya ce Gwamna Lawal bai gudu daga jihar ko kasar ba.
Ya ce sabanin zargin Mista Matawalle, Gwmanan ya fita kasar ne domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.
Masu garkuwa sun sace daliban jami'ar Gusau
Kun ji cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a daren jiya da misalin karfe uku na dare kamar yadda aka tabbatar a yau Juma'a 22 ga watan Satumba, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng