Innalillahi: Jarirai 5 Sun Mutu a Hannun 'Yan Bindiga Kwanaki Kadan Bayan Sace Su

Innalillahi: Jarirai 5 Sun Mutu a Hannun 'Yan Bindiga Kwanaki Kadan Bayan Sace Su

  • Ana cikin tashin hankali bayan mutuwar jarirai guda biyar a hannun 'yan bindiga a jihar Kaduna bayan sun sace su
  • Kimanin wata daya kenan da maharan su ka kai hari a yankin Birnin Gwari da ke jihar tare da sace mata ma su shayarwa
  • Shugaban matasa a yankin Rangadi, Shehu Rangadi ya bayyana irin matsalar da su ka shiga na siyar da kadarorinsu don biyan kudaden

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Kimanin wata guda kenan da 'yan bindiga su ka kai hari yankin Birnin Gwari inda su ka sace mutane da dama ciki har da mata.

Daga cikin wadanda maharan su ka sace mutum 17 akwai mata ma su shayarwa da jariransu yayin farmakin.

Kara karanta wannan

Satar mazakuta: tsagera sun yi wa lakcara dukan kawo wuka a jihar Arewa, 'yan sanda sun fusata

Akalla jarirai biyar ne su ka mutu a hannun 'yan bindiga a Kaduna
'Yan bindiga sun addabi yankunan karkara a jihar Kaduna. Hoto: Punch.
Asali: UGC

Yaushe aka sace mutanen da ya yi sanadin jariran?

Jarirai biyar daga cikinsu sun rasa ransu duk da karbar kudin fansa da maharan su ka yi na naira miliyan 19.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun nemi kudin fansa miliyan 19, bayan sun karba sai su ka sake mutane hudu kacal tare da bukatar karin kudin fansar.

Wani shugaban matasa a yankin Rangadi mai suna Shehu Rangadi ya tabbatar wa Aminiya cewa maharan ne su ka kira su a waya don sanar da su mutuwar yaran.

Mene sanadin mutuwar jariran a hannun 'yan bindiga?

Ya ce 'yan bindigar sun tabbatar musu da cewa rashin lafiyar iyayensu mata ne ya hana su shayar da yaran har su ka rasa ransu.

Shehu ya bayyana irin tashin hankali da su ka shiga kan neman kudin fansa inda ya ce har kadarorinsu su ka siyar don biyan kudaden.

Kara karanta wannan

Mutum 1 ya rasa ransa inda wasu 5 su ka raunata a rikicin zaben ma su gidan haya, an tafka asara

Ya kara da cewa a daren ranar Talata 7 ga watan Nuwamba, 'yan bindigan sun sa ke kai hari kauyen Algaita tare da sace mutane 12 ciki har da mata.

Sojoji sun hallaka kwamandan 'yan bindiga

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka wani kwamandan 'yan bindiga a jihar Kebbi.

Kasurgumin dan bindigan mai suna Mainasara ya rasa ransa ne bayan samamen da rundunar ta kai a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.