Dakarun Soji Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Sarkin Fulani a Filato

Dakarun Soji Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Sarkin Fulani a Filato

  • Dakarun soji da ke atisayen Safe Haven (OPSH) sun samu nasarar kamo wanda ake zargi da kashe Adamu Gabdo, sarkin al'umar Fulani makiyaya a Filato
  • A watan Satumba ne aka kashe Gabdo, a yankin garin Panyam, karamar hukumar Mangu ta Filato, inda daga bisani rundunar sojin ta fara farautar makashin
  • Dakarun sojin OPSH sun bi sawun wanda ake zargin zuwa Legas tare da kama shi a gidan kallon kwallo, bayan kwashe makonni suna farautarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Hukumar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama Philip Gokas, wanda ake zargi da kashe Adamu Gabdo, Sarkin al'umar Fulani makiyaya a jihar Filato.

A ranar 23 ga Satumba, aka kashe Gabdo, Sarkin Fulani na garin Panyam, a yankin da ke a karamar hukumar Mangu ta Filato.

Kara karanta wannan

Umar Ka'oje: Farfesan Najeriya ya mayar da fiye da miliyan 1 da aka tura masa bisa kuskure

Philip Gokas
Dakarun sojin sun kama Philip Gokas a wani gidan kallon kwallo yana shan giya, a Legas Hoto: Nigerian Army
Asali: Facebook

Bayan wasu kwanaki, Taoreed Lagbaja, babban hafsan soji (COAS) ya umurci jami’an sojin na Safe Haven (OPSH) da su kamo wadanda suka kashe Gabdo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama Philip Gokas a Legas

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Larabar da ta gabata, hukumar sojin Najeriya ta ce sojojin OPSH sun bi sawun wanda ake zargin zuwa yankin Ogba da ke Legas, bayan kwashe makonni suna farautarsa.

A cewar sanarwar, an kama Gokas ne a wani gidan kallon kwallon kafa inda yake shan giya, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Hukumar ta bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin kashe Gabdo.

Sanarwar ta ce:

"Kame Mista Philip Gokas wanda aka fi sani da Jaykimo a jihar Legas ya biyo bayan farautar makwanni da dakarun suka yi domin gurfanar da mai laifin a gaban kuliya."

Kara karanta wannan

An Kama Mutane 4 Kan Laifin Satar Kujerar Bandaki Na Gwal Daga Fadar Blenheim

“Bisa bin diddigin da dakarun OPSH su ka yi ne ya sa aka gano inda ya ke, sannan aka kama shi a unguwar Ogba da ke jihar Legas, inda aka same shi yana jin dadi da shan giya a wani gidan kallon kwallon kafa.

Gokas ya amsa laifin kashe shugaban Fulani

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Kame Mista Philip Gokas shaida ne ga jajircewa da sadaukarwar da dakarun OPSH su ka yi da kuma tasirin kokarin hadin gwiwa na fannoni daban daban.
"Mista Gokas ya amince da aikata laifin, sannan ya bayar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen kama wasu mutanen da ke da hannu a wannan danyen aikin nan da kwanaki masu zuwa."

Kungiyar Fulani ta yi martani kan kisan musulmai a Jos

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah wadai da harin kwanton bauna da kashe matafiya da wasu 'yan ta'adda suka yi a hanyar Rukuba a garin Jos, jaridar Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel