Emefiele: Kotu Ta Cimma Matsaya Kan Tsohon Gwamnan CBN Bayan Mika Shi da EFCC Ta Yi
- Daga karshe, babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Alkalin kotun, Olukayode Adeniyi shi ya ba da umarnin ga Gwamnatin Tarayya inda ya ce ta sake Emefiele ga lauyoyinsa
- Wannan hukunci na zuwa ne bayan korafin da tsohon gwamnan na CBN, Emefiele ya shigar a gaban kotun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Yayin shari'ar, Alkalin kotun, Olukayode Adeniyi ya ba da umarni ga Gwamnatin Tarayya da ta sake Emefiele zuwa ga lauyoyinsa.
Wane hukunci kotun ta yanke kan Emefiele?
Wannan hukunci na zuwa ne bayan korafin da tsohon gwamnan na CBN, Emefiele ya shigar a gaban kotun, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yau Laraba ce hukumar EFCC ta bi umarnin kotun inda ta mika tsohon gwamnan ga kotun da ke zamanta a Abuja.
Kotun a ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba ta umarci hukumar EFCC ta sake Emefiele don mika shi ga kotun, Vanguard ta tattaro.
Wane zarge-zarge ake yi kan Emefiele?
Daga bisani hukumar EFCC ta bi umarnin kotun wurin mika shi ga babbar kotun Tarayya da ke zamanta Abuja a yau Laraba 8 ga watan Nuwamba.
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele makwanni kadan bayan hawanshi karagar mulki.
Akwai korafe-korafe da dama kan Emefiele musamman a badakalar makudan kudade yayin da ya ke mulkin bankin.
Har ila yau, ana zargin Emefiele da daukar nauyin ta'addanci a kasar da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama.
EFCC ta mika Emefiele a gaban kotu
A wani labarin, hukumar EFCC ta bi umarnin kotun inda ta mika tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele a yau.
Hukumar EFCC ta kama Emefiele ne awanni kadan bayan hukumar DSS ta sake shi a Abuja a makon da ya gabata.
Wanna na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shari'ar tsohon gwamnan CBN din kan wasu zarge-zarge a kansa.
Asali: Legit.ng