Babban Labari: Farashin Litar Man Fetur Ya Ƙara Tashin Gwauron Zabi a Jihar APC, An Shiga Wani Hali

Babban Labari: Farashin Litar Man Fetur Ya Ƙara Tashin Gwauron Zabi a Jihar APC, An Shiga Wani Hali

  • An wayi gari da ƙarin farashin litar man fetur a jihar Imo yayin da NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki a faɗin ƙasa
  • Matafiya sun shiga mawuyacin hali yayin da litar mai ta tashi daga N650 zuwa N700 a jihar da ke Kudu maso Gabas
  • Dillalan fetur a titin Owerri zuwa Aba sun ce tashin farashin ba shi da alaƙa da yajin aikin NLC, dala ce ta jawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Rahotanni daga jihar Imo da ke Kudu maso Gabshin Najeriya sun nuna cewa farashin man fetur ya tashi daga N650 zuwa N700 a kowace lita.

Farashin man fetur ya ƙara tashi a Imo.
Matafiya Sun Shiga Mawuyacin Hali Yayin da Farashin Litar Man Fetur Ya Ƙara Tashi a Jihar APC Hoto: NNPC
Asali: UGC

Wannan tashin farashin litar fetur a lokaci guda ya ƙara jefa matafiya cikin mawuyacin hali a daidai lokocin da suke fafutukar jure ƙarin farashin farko.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo: Akwai yiwuwar ba za a yi zabe ba bayan an samu sabani kan muhimmin abu 1

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito sabon ƙarin ya yi wa matafiya ba zata duk da kokarinsu na juriya kan tashin farashin farko da aka nunnunka farashin lita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya haddasa sabon ƙarin?

An tattaro sabon ƙarin da aka samu a farashin litar man fetur ɗin ya samo asali ne daga abubuwa da dama ciki har da barazanar ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC).

Ƙungiyar NLC ta yi barazanar dakatar da safarar man fetur zuwa jihar Imo, wanda hakan na cikin dalilan da ake tunanin ya haddasa tashin farashin a lokaci ɗaya.

Amma wasu dillalan man fetur a kan titin Owerri zuwa Aba sun bayyana cewa ƙarin kuɗin da aka samu ba shi da alaƙa da yunƙurin NLC na shiga yajin aiki a jihar Imo.

A cewarsu, sabon karin ya samo asali ne daga tashin farashin canza dala da Naira wanda a yanzu ya haura N1000 kan kowace dala ɗaya, kamar yadda The Sun ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

"Saboda haka ba shi da alaƙa da ƙungiyar kwadago NLC," in ji wata majiya a cikin dillalan man fetur.

Wani mai aiki a gidan mai, Kabiru Mai Fetur, ya faɗa wa Legit Hausa cewa tun kafin ma'aikata su bayyana shirin shiga yajin aiki lita ta ƙara tsada a gidajen mai.

"Tun mako ɗaya da ya wuce zuwa biyu, litar mai ta tashi daga N620, mu dai yanzu muna sayar da shi N630 zuwa N640, ya danganta da yadda ya iso wajen mu."
"Saboda haka nima ina ganin ƙarin ba shi da alaƙa da NLC, sai dai tabbas idan wannan yajin aiki ya tabbata, to fa za a shiga sabuwar matsala da ka iya tashin farashin."

Jirgin Ruwa Ya Gamu da Mummunan Hatsari

A wani rahoton na daban Jirgin ruwa ya ƙara gamuwa da hatsari a jihar Nasarawa ranar Litinin, aƙalla mutane huɗu sun riga mu gidan gaskiya.

Ganau ya bayyana cewa waɗanda suka mutu suna hanyar zuwa taimaka wa ɗan uwansu a aikin gona lokacin da lamarin ya rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262