Mutum 1 Ya Rasa Ransa inda Wasu 5 su ka Raunata a Rikicin Zaben Ma Su Gidan Haya, an Tafka Asara

Mutum 1 Ya Rasa Ransa inda Wasu 5 su ka Raunata a Rikicin Zaben Ma Su Gidan Haya, an Tafka Asara

  • Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta tabbatar da yamutsin da ya afku a jihar kan zaben shugabancin ma su gidajen haya
  • Yayin hatsaniyar wani ya rasa ransa yayin da mutane biyar su ka jikkata da kuma samun asarar dukiyoyi na gidaje da kuma ababen hawa
  • Kakakin rundunar a jihar, Ikenga Tochukwu shi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce jami’an sun dauki kwararan matakai kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra – Wani matashi ya rasa ransa yayin da wasu biyar su ka samu raunuka a wani hargitsi na neman shugabanci a jihar Anambra.

Wannan lamari ya faru ne yayin da ake zaben shugabannin ma su gidajen haya a karamar hukumar Ogbaru da ke jihar.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

An rasa rayuka yayin rikicin zaben ma su gidajen haya a Anambra
'Yan sanda sun yi martani kan rasa dukiyoyi a Anambra. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Wane asara aka tafka yayin rikicin a Anambra?

Akalla an lalata ababen hawa fiye da 30 da gidaje fiye da 20 da lissafinsu ya kai naira miliyan 100 yayin rikicin, Ripples ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa rikicin ya fara ne yayin da matasan ke zargin wadanda ba ‘yan asalin jihar ba sun gudanar da zaben shugabannin a yankin.

Hakan ya sabawa zaben da asalin ‘yan jihar su ka yi a makon da ya gabata wanda hakan ya jawo rudani a kungiyar ta ma su gidajen haya.

Wane maryani ‘yan sanda su ka yi kan rikicin?

A zaben da aka gudanar na wadanda ba ‘yan jihar ba, Sunday Obinze ya yi nasara a matsayin shugaba wanda hakan bai yi wa wasu dadi ba.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Ikenga Tochukwu ya ce jami’ansu sun dauki mataki kan wannan lamari da ya faru, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Mai magani ya dirkawa wani harsashi har lahira yayin gwada maganin bindiga a Bauchi

Tochukwu ya kara da cewa sun dauki wadanda su ka ji raunuka zuwa asibiti mafi kusa don ba su kulawa ta musamman.

Fasto a Anambra ya yi barazanar makantar da mutane

A wani labarin, Wani shahararren Fasto mai suna Chukwuemeka Odumeji ya yi barazanar makantar da Fastoci ma su ta ya Isra’ila addu’a.

Faston ya ce idan ba rashin sanin ciwon kai ba, ta yaya za su tsallake matsalolin Najeriya su je su na yi wa Isra’ila addu’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.