Yada Bidiyon Tsiraici: Kotu Ta Daure Mutum 5 Kan Laifin Damfarar Tsohon Kakakin Majalisa Miliyan 38

Yada Bidiyon Tsiraici: Kotu Ta Daure Mutum 5 Kan Laifin Damfarar Tsohon Kakakin Majalisa Miliyan 38

  • Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar ga wasu mutane biyar da aka kama da laifin yada bidiyon tsiraicin tsohon kakakin majalisar jihar Osun, Tomothy Owoeyo
  • Hakazalika kotun ta kama mutanen da laifin yin amfani da bidiyon wajen damfarar dan siyasar naira miliyan 38 a shekarar 2018
  • Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da, Kazeem Agbabiaka, Rasheed Ojonla, Babatunde Oluajo, Adebiyi Kehinde, Femi Oseni, da kuma Oyebanji Oyeniyi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Osogbo, jihar Osun - Mai Shari'a Nathaniel Ayo-Emmanuel na babbar kotun tarayya da ke Osogbo, jihar Osun, a ranar Talata, ya yanke wa wasu mutane biyar hukuncin daurin shekaru biyar sakamakon kama su da laifin yada bidiyo da kuma damfarar tsohon kakakin majalisar jihar Osun, Timothy Owoeyo.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa mutum 6 hukunci kan damfarar kakakin majalisa N38m

A cikin shekarar 2018, wani bidiyo mai tsawon dakiku 13 na tsiraicin Owoeye ya zagayer intanet, inda matasan suka damfari tsohon kakakin majalisar naira miliyan 38.

Timothy Owoye
Kotu ta daure mutane biyar akan laifin damfarar tsohon kakakin majalisa N38m Hoto: Timothy Owoye
Asali: Twitter

A cikin bidiyon, an nuna wasu mutane na cin zarafi da tusa keyar Owoeye, bisa zarginsa da zuwa garinsu don gudanar da ayyukan tsafi, kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta cafke mutanen da ke cikin bidiyon, wadanda aka yi zargin sun yi amfani da bidiyon wajen damfarar Owoeye naira miliyan 38, kafin daga bisani suka wallafa bidiyon a intanet.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da, Kazeem Agbabiaka, Rasheed Ojonla, Babatunde Oluajo, Adebiyi Kehinde, Femi Oseni, da kuma Oyebanji Oyeniyi, kuma an gurfanar da su gaban kotun ne a ranar 19 ga watan Oktoba, 2018, akan laifuka biyar da suka shafi hada kai don aikata laifi, damfara, yada bidiyon tsiraici, da sauransu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga babbar matsala, masu ruwa da tsakin PDP sun goyi bayan Ministan Tinubu

Hukuncin da kotu ta yanke

Da ya ke yanke hukunci kan karar, Mai Shari'a Ayo-Emmanuel ya ce wadanda ake tuhuma na aiki ne kamar 'yan fashi a yanar gizo, inda su ke jefa abin harinsu cikin kuncin rayuwa, don haka ba sa bukatar sassauci daga kotu.

A karshe ya yanke wa Agbabiaka, Oyeniyi, Ojonla da Oluajo shekaru biyar a gidan gyaran hali bisa kamasu da laifin hada kai don aikata laifi da kuma damfara ta yanar gizo.

Sai dai, mai shari'ar, ya wanke tare da sallamar Ismaila Azeez, akan laifin da ake tuhumarsa na bin diddigi da yada bidiyon a intanet, amma ya yanke wa Oseni hukuncin shekaru biyar a gidan gyara hali ga Oseni akan irin laifin da aka tuhumi Azeez.

Yadda na tsira daga harin kisan kai - Timothy Owoeyo

Kunji yadda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Timothy Owoeye, ya bayyana yadda ya tsira daga harin yan daban siyasa da suka yi yunkurin kashe shi a Ilesa da ke mazabar Sanatan Osun ta gabas.

Wannan harin, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito na zuwa ne yayin da manyan jam'iyyu All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) ke musayar yawu suna zargin juna da kisan mambobinsu a garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.