A Shirya: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Mamayar Da Tinubu Zai Yi Wa 'Yan Boye Dala

A Shirya: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Mamayar Da Tinubu Zai Yi Wa 'Yan Boye Dala

  • Bankin CBN da Fadar shugaban kasar Najeriya sun tsaya tsayin-daka saboda darajar Naira ta mike a kasuwar canji
  • Dr. Tope Fasua ya ja-kunnen wadanda ke yawan boye kudin waje cewa za a mamaye su, ana son cin riba a araha banza
  • Hadimin shugaban kasar ya fara hango haske a tafiyar gwamnatinsu, ya na tunani Dala za ta rasa daraja a kasuwa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Fadar shugaban kasa ta shaida cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa za su yi kokarin karfafa darajar Naira.

A ranar Talata Tribune ta rahoto Dr Tope Fasua ya na cewa za a fito da tsare-tsaren tattalin arziki da za su jawo a karfafa kudin Najeriya.

Kara karanta wannan

Manufofin CBN da Tinubu sun fara aiki, naira za tayi daraja, Sanatan PDP

Tope Fasua shi ne wanda aka nada ya ba shugaban kasa shawarar tattalin arziki.

Tinubu
Bola Tinubu zai so Naira ta yi daraja Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naira ta mike a kasuwar canji

Masanin tattalin ya yi jawabi ne a wajen wata lacca da liyafa ta musamman da aka shirya mai taken “Cowries to Cash” a birnin tarayya Abuja.

Fasua ya ce a kwanakin baya-bayan nan, Naira ta tashi a kasuwar canji, ya kuma ce manufofinsu za su jawo kudin ya cigaba da kara yin daraja.

"Idan dai ana so a ruguza duk wata kasa, Fasua ya ce ana farawa ne da darajar kudinta.

- Dr. Tope Fasua

Naira za ta ba 'Yan Najeriya mamaki

Daily Trust ta ce hadimin shugaban kasar ya gargadi masu boye kudin kasashen waje da nufin Naira ta karye, yake cewa za su sha mamaki.

Kara karanta wannan

Barayi sun sacewa Najeriya man fiye da Naira Tiriliyan 4.3 a shekaru 5 Inji NEITI

A cewar Dr. Fasua, tsare-tsaren da gwamnati mai-ci ta fito da su, za su girgiza masu dankara kudin waje saboda son cin riba a banza kurum.

Mai ba shugaban kasa shawara ya halarci taron ne a madadin Mai girma Kashim Shettima.

"Masu hari da addu’a kudinsu ya zama na banza, na yi imanin cewa tsare-tsaren da CBN da gwamnatin da na ke yi wa aiki, a karkashin jagorancin shugaban kasa, zai girgiza wasu daga cikinsu.
Ku na bukatar sauraron manufofin, shi kan shi mutumin (Tinbu) kuma za ku ga matakin da yake tunani ya sha gaban mafi yawanmu.

- Tope Fasua

Ya darajar Naira a kan Dalar Amurka

A ‘yan kwanakin nan, Naira ta na ta tangal-tangal bayan wani mummunan tashin da Dalar Amurka da sauran kudin kasashen ketare su ka yi.

Shi Fasua ya na ganin nan gaba Dalar Amurka za ta iya saukowa zuwa N600 ko N500.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng