Dakarun Sojoji Sun Sheke Ƴan Ta'adda 10 a Kaduna, Sun Kwato Makamai Masu Yawa

Dakarun Sojoji Sun Sheke Ƴan Ta'adda 10 a Kaduna, Sun Kwato Makamai Masu Yawa

  • Dakarun sojoji na runduna ta ɗaya a jihar Kaduna, sun samu nasarar sheƙe miyagun ƴan ta'adda 10
  • Haziƙan dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'addan ne a cikin mako guda a yayin arangamar da suka yi da su a sassa daban-daban na jihar
  • A yayin fafatawar dai dakarun sojojin sun ƙwato makamai masu yawa ta baburan da ƴan ta'addan su ke amfani da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojoji na runduna ta ɗaya da 'Operation Whirl Punch' sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda 10 da ƙwato makamai masu yawa a cikin mako ɗaya.

A cewar wata sanarwa da muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ya ce dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda huɗu a wani samame da suka kai a ƙauyen Kamfanin Doka cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a ranar 1, ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun halaka dan kasuwa da sace manoma 4 a Borno

Dakarun sojoji sun halaka ƴan ta'adda
Dakarun Sojoji sun sheke ƴan bindiga 10 a Kaduna Hoto: Patrick Meinhardt/AFP
Asali: Getty Images

A yayin samamen, sojojin sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya, jigidar AK47 guda ɗaya, adda ɗaya, wayar hannu ɗaya da kuma babura 14 daga hannun ƴan ta'addan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojojin suka fatattaki ƴan ta'adda

Haka kuma a ranar 2 ga Nuwamba, 2023, sojojin sun halaka ɗan bindiga ɗaya a ƙauyen Sabon Sara bayan wasu manoma sun kawo musu bayanin ƙoƙarin farmakarsu da ƴan bindiga suka yi a gonakinsu.

Sojojin sun ƙwato bindigu ƙirar AK47 guda biyu yayin da ɗaya daga cikin manoman mai suna Malam Abdulrahman Aliyu wanda ya samu ƙananan raunuka a yayin arangamar, aka ɗauke shi zuwa wani asibitin sojoji da ke kusa domin yi masa magani.

Hakazalika, a ranar 3 ga Nuwamba, 2023, bisa ga sahihan bayanan sirri, sojoji sun gudanar da aikin share fage a yankunan Kankomi, Juji, Gwantu, Kujeni, Kikwari da Kaso, duk a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Hare-haren sojojin sama sun halaka ƴan ta'adda masu yawa a yankuna 2 na Arewacin Najeriya

Ya ce sojojin sun yi arangama da ƴan bindiga inda suka yi nasarar kashe biyu daga cikinsu tare da ƙwato bindiga kirar AK47 guda ɗaya, jigidar AK47 ɗaya, harsashi na musamman mai kaurin 7.62mm guda huɗu, babur Honda ɗaya da wayar hannu ɗaya.

Har ila yau, a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2023, yayin da ake cigaba da wani aikin share fage a ƙauyukan Maidaro, Ngade, Ahla da Rikau a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar, sojojin sun yi arangama da ƴan ta'adda.

Ya ce sojojin sun halaka biyu daga cikin ƴan ta'addan yayin da sauran suka tsere da harbin bindiga sannan suka bar babur ɗaya

Hakazalika ya ce, a wannan rana, sojoji sun kai wani samame a kewayen Tantatu da Antena a ƙaramar hukumar Chikun inda suka yi nasarar kashe wani ɗan ta’adda guda daya da ƙwave bindiga kirar AK47 ɗaya, jigidar AK47 daya, harsasai mai kairin 7.62mm guda bakwai da wayoyin hannu guda biyu.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun halaka ƴan bindiga masu yawa a Zamfara yayin dakile wani kazamin hari

Sojoji Sun Sheke Ƴan Binɗiga a Zamfara

A wani labarin kuma, dakarun sojoji sun samu nasarar sheƙe ƴan bindiga masu yawa a wata fafatawa da suka yi a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin dai sun daƙile wani kwanton ɓauna da ƴan bindigan suka yi musu ne a ƙauyen Karazau na ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng