“Ina Ta Mugayen Mafarkai”: Budurwa Ta Koka Bayan Ta Farke Matashin Kai da Ta Siya N800

“Ina Ta Mugayen Mafarkai”: Budurwa Ta Koka Bayan Ta Farke Matashin Kai da Ta Siya N800

  • Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta baje kolin abubuwan da ta gano a cikin matashin kai ta siya
  • Matashiyar ta koka sannan ta bayyana cewa ta siya katifar kan N800 daga wajen wani bahaushe amma bata fadi dalilin da yasa take so ta rabu da shi ba
  • A cikin bidiyon, matashiyar ta fito da matashin sannan ta zazzage abun da ke ciki kafin ta cinna masa wuta a harabar gidanta

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiya yar Najeriya ta koka a soshiyal midiya bayan ta ga abubuwan da ke cikin matashin kanta.

A cikin bidiyon da ya yadu, @chubby_folly, ta bayyana cewa ta siya matashin akan N800 daga wajen wani mallam bahaushe.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Matashiya ta koka bayan farke matashin kai da ta siya
“Ina Mugayen Mafarkai”: Budurwa Ta Koka Bayan Ta Farke Matashin Kai da Ta Siya N800 Hoto: @chubby_folly
Asali: TikTok
"Gaba daya wadannan abokin basu da rayuwa," @chubby_folly ta koka yayin da ta yada bidiyon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiyar ta fito da matashin kan sannan ta yaga shi don nuna abubuwan da ke ciki kafin ta kona shi.

Wasu mutane sun caccake ta, suna mamakin abun da take tsammani bayan ta siya matashin kai mai arha.

Ga bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan matashin kanta

user8748165701206 ya ce:

"Na siya zanin gado sannan ya fada mani 6*6 ne… kawai sai na je gida na ga kwali ne a ciki yanzu ina daura shi ne kamar zani."

Flashy_empress ta ce:

"Na siya matashin kai daga wajensu bayan mijina ya gargade ni, wari ya so kashe mu a wannan rana ya jefar da shi cikin fushi."

Jhudeewealth ta ce:

"Na siya zanin gado, ya yi mani alkawarin cewa babban gado ne kawai sai na isa gida na tarar da zanin gadon karamin gado a gefen kwalaye."

Kara karanta wannan

Wata mata ta yi yaji bayan sun samu sabani da mijinta, ya je biko da tsinken tsire 2

Pearly ta ce:

"Na siya irinsa shekaru 4 da suka wuce, ina ta mugayen mafarkai sai da na bude don ganin abun da ke ciki, nima kona shi na yi."

Wani mutum ya zuba man ja a mota

A wani labarin, mun ji cewa jama'a sun yi cece-kuce a kan wani bidiyon TikTok da ya yadu wanda ke nuna yadda aka yi amfani da man ja a madadin man injin din mota.

A cikin dan gajeren bidiyon, mutumin ya juye galan din man ja a cikin injin din motar a wani wuri da ke kama da wajen gyaran motoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng