Tsohuwar shugabar ma’aikatan tarayya Oyo-Ita ta isa kotun Abuja da matashin kai (hotuna)

Tsohuwar shugabar ma’aikatan tarayya Oyo-Ita ta isa kotun Abuja da matashin kai (hotuna)

- Tsohuwar shugabar ma’aikatan tarayya, Oyo-Ita wacce hukumar EFCC ta gurfanar kan zargin zamba ta isa babbar kotun tarayya da ke Abuja don shari’a

- Jami’an hukumar yaki da rashawar sun kawo Oyo-Ita kotu a Abuja a ranar Litinin, 23 ga watan Maris

- An gurafanar da tsohuwar shugabar ma’aikatan ne tare da wasu mutum takwas a gaban Justis Taiwo Taiwo

Tsohuwar shugabar ma’aikatan tarayya, Oyo-Ita, wacce hukumar EFCC ke bincika kan zargin hamdame kudade ta isa babbar kotun tarayya a Abuja a ranar Litinin, 23 ga watan Maris, dauke da matashin sanya kai.

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta kawo Oyo-Ita zuwa babbar kotun tarayya a Abuja a safiyar ranar Litinin kan zargin zamba.

Tsohuwar shugabar ma’aikatan tarayya Oyo-Ita ta isa kotun Abuja da matashin kai (hotuna)

Tsohuwar shugabar ma’aikatan tarayya Oyo-Ita ta isa kotun Abuja da matashin kai
Source: Twitter

Za a gurfanar da ita tare da wasu mutum takwas a gaban Justis Taiwo Taiwo.

Hukumar EFCC ta ce bincike ya nuna cewa a lokacin da ta ke a matsayin darakta, sakatariyar din-din-din da shugabar ma’aikata, Oyo-Ita ta yi amfani da kamfanoninta da shigewa gaba wajen karban kwangiloli daban-daban a ma’aikatu da hukumomin daban-daban da take aiki.

Tsohuwar shugabar ma’aikatan tarayya Oyo-Ita ta isa kotun Abuja da matashin kai (hotuna)

Tsohuwar shugabar ma’aikatan tarayya Oyo-Ita ta isa kotun Abuja da matashin kai (hotuna)
Source: UGC

Ana kuma zargin Oyo-Ita da yi ikirarin bogi na kagaggun DTA, kudaden taro wanda gwamnati ta biya asusun wadanda ake zargi da taimakon hadiminta na musamman.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Shugaban CAN ya ce mugunta da laifuffukan jama’a ne ya haifar da annobar

A wani labari na daban mun ji cewa, Gwamnatin tarayya ta dage dokarta ta haramta kaiwa garuruwan da ke kusa da iyakokin kasar nan man fetur.

Idan zamu tuna, a ranar 6 ga watan Nuwamban 2019 ne kwamitin kula da iyakokin kasar nan wanda shugaban hukumar kwastam ta a kasa, wacce Hameed Ali ke shugabanta, ya haramta kai dukkan kayayyakin man fetur gidajen mai da ke da nisan kilomita 20 zuwa iyakokin kasar nan.

Amma kuma, bayan watanni hudu da wannan dokar, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar dage dokar ta hanyar amincewa gidajen mayuka 66 a yankunan, samar da man fetur.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel