Kano: Hisbah Ta Yi Martani Kan Aske Kan Wata Budurwa da Kwalba, Ta Fadi Matakin da Ta Dauka a Kai
- Hukumar Hisbah ta yi martani kan zargin aske kan wata budurwa da ake yi yayin wani samame
- Hukumar ta bakin kwamandanta, Sheikh Aminu Daurawa ya yi karin harke kan zargin da ake yi
- Daurawa ya ce bidiyon da aka wallafa babu kamshin gaskiya a cikinsa inda ya ce za su dauki mataki
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Hukumar Hisbah a jihar Kano ta musanta zargin aske gashin ‘yan mata da ta kama a otal otal yayin ran gadi.
Rundunar a kwanakin nan ta kai samame don kawar da badala a cikin shirinsu na ‘Operation Kau da Badala’ a jihar baki daya.
Mene ake zargin Hisbah da yi?
Yayin samamen, rundunar ta kama wasu wadanda ake zargi da dama a otal otal da wuraren shakatawa wanda ya jawo kace-nace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa faifan bidiyo inda ya ke zargin cewa hukumar ta kama wata budurwa a otal tare da aske mata kai.
A cikin faifan bidiyon, ana zargin an yi wa budurwar wacce ba ‘yar Kano ba ce aski da kwalba.
Wane martani Hisbah ta yi kan zargin?
Yayin da ta ke martani a yau Talata 7 ga watan Nuwamba, hukumar ta bayyana faifan bidiyon da kage don bata mu su suna, cewar Newstral.
Kwamnadan Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa shi ya bayyana haka inda ya ce babu wani abu makamancin haka da ya faru.
Daurawa ya ce Hisbah na aiwatar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanadar ba tare da tauye wa kowa hakki ba.
Ya ce a halin yanzu hukumar ta gano wanda ya wallafa bidiyon inda ya ce za su gayyace shi don yin bayani da kare kansa.
Ya kara da cewa idan har wanda ake zargin ya gagara kare kansa, to ba su da wata zabi illa daukar mataki a kansa, cewar Daily Trust.
Daurawa ya kara da cewa tabbas akwai kura-kurai yayin aiwatar da ayyukan hukumar, amma ta dauki matakin kare faruwar hakan nan gaba.
Hisbah ta shirya aurar da Murja
Kun ji cewa, hukumar Hisbah a Kano ta shirya aurar da shaharriyar ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.
Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ta gayyaci dukkan ma su amfani da manhajar don samun maslaha.
Asali: Legit.ng