Sanata Imasuen Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Sanatocin Labour Party Ba Za Su Hana Siyo Motocin N160m Ba

Sanata Imasuen Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Sanatocin Labour Party Ba Za Su Hana Siyo Motocin N160m Ba

  • Sanata Neda Imasuen ya ce ƴan Najeriya na sukar ƴan majalisar LP bisa rashin adalci saboda rashin ƙin amincewa da shirin sayen motocin alfarma
  • Imasuen ya ce ƴan majalisar LP sun yi kaɗan da hana shirin siyan motocin SUV ga ƴan majalisu
  • A cewar sanatan na LP, Imasuen ya ce ba a ba shi wata mota ba kuma ba yi masa tayin hakan ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Birnin Benin, jihar Edo - Sanata mai wakiltar Edo ta tsakiya, Neda Imasuen, na jamviyyar Labour Party, ya ce jam'iyyar adawa ba za ta iya dakatar da shirin da majalisar tarayya ta ƙasa ta yi na sayen motocin (SUV) da kuɗinsu sun kai N160m ga kowane ɗan majalisa ba.

Kara karanta wannan

"Ba zan taba daina kiran Tinubu dillalin kwayoyi ba", Datti Baba-Ahmed ya bayar da dalili

Imasuen ya ce rashin adalci ne ƴan Najeriya su soki ƴan majalisar LP saboda rashin ƙin amincewa da shirin, cewar rahoton The Punch.

Sanata Imasuen ya yi magana kan siyo motocin N160m
Sanata Imasuen ya ce ƴan majalisun LP ba zu iya hana siyo motocin N160m ba Hoto: @SenNedaImasuen
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa ƴan majalisar LP a majalisar tarayya sun yi kaɗan da hana shirin sayen motocin na alfarma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ƙarshen mako a birnin Benin, babban birnin jihar Edo.

Meyasa sanatocin LP ba za su iya hana siyo motocin ba?

Kamar yadda BusnessDay ta ruwaito, Imasuen ya lura cewa sanatocin LP takwas ba za su iya sa yawancin ƴan majalisar su ja da baya kan shirin siyan motocin na alfarma ba.

A kalamansa:

“Ina so na faɗa cewa ban karɓi wata mota ba kuma babu wacce aka yi min tayin ta. Duk da haka, muna cikin dimokuradiyya inda mafi rinjaye ke yin galaba yayin da marasa rinjaye kuwa sai dai su faɗi ra'ayinsu."

Kara karanta wannan

Nasarar Tinubu: Peter Obi ya yanke shawara kan sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027

"Mu kawai za mu iya cewa abin da muka yi amanna shi ne abin da ya dace a yi a majalisa. Mu sanatoci takwas ne kawai, a cikin Sanatoci 109. Domin haka, waɗanda suka mayar da hankalin kan sanatocin Labour Party, ina ganin hakan rashin adalci ne sosai."
"Mu ɗauka cewa an ba sanatoci 109 motoci sannan sai takwas daga ciki suka ƙi karɓa, za ku iya gayamin amfanin hakan ga kasafin kuɗi ko ƙimar majalisar tarayya?"

Martanin Shehu Sani ga LP Kan Siyo Motocin N160m

A wani labarin kuma, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi martani bayan jam'iyyar Labour Party ta buƙaci mambobinta da kada su karɓi motocin N160m.

Shehu Sani ya yi nuni da cewa babu ɗaya daga cikin ƴan majalisun wanda zai haƙura ya ƙi karɓar motocin na alfarma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng