FG Ta Kashe Biliyan 90 Kan Tafiye-Tafiyen Shugaban Kasa Cikin Shekara 9, Sabon Bincike
- A cikin shekaru tara kawai, rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta kashe akalla Naira Biliyan 90 akan tafiye-tafiyen shugaban kasa ta jiragen sama
- A mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, an kashe akalla naira biliyan 61.42 a tafiye tafiyen da ta yi tsawon wa'adin mulkinsa na shekaru takwas
- A mulkin gwamnatin Tinubu kuwa, a shekarar 2023 kawai, an kashe akalla naira biliyan 25.7 a tafiye tafiyen da shugaban ya yi ta jiragen sama
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Batu kan irin makudan kudaden da ake ware wa bangaren tafiye tafiyen shugaban kasa a jiragen sama ya fara tayar da hazo, inda cikin shekaru tara aka kashe akalla naira biliyan 90 kan sufurin shugaban kasa a jirgin sama.
Kara yawan kudin a cikin kasafin kudin kasa ya jawo muhawara mai zaifi, da ya kai ga har an fara bin ba'asin sanin manufar gwamnati kan kudaden da ake kashewa a kasar, da kuma sanin abin da ta ke yi na alkinta kudaden jama'a.
Misali, a shekaru hudun farko na tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, an ware naira biliyan 20.42 don sufurin shugaban kasar a jirgi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin mamaki, kudin da aka ware a wa'adin mulkinsa na biyu na rubanya na farko, inda ya kai naira biliyan 41.
Kasafin kudin tafiye tafiyen Tinubu a jiragen sama
A makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da karashen kasafin kudin 2023 ga majalisar tarayya, inda aka ware naira biliyan 12.7 domin sufurin shugaban kasar a jirgi karkashin ofishin mai tallafa wa shugaban kasar ta fuskar tsaro.
Idan aka hada da kudin da aka fara ware wa a kasafin kudin shekarar na farko da ya kai naira biliyan 13, ya tashi Naira Biliyan 25.7 kenan.
Shugaban kasar na tafiye tafiye a cikin rukunin jiragen da aka fi sani da Nigeria Air Force One, da suka hada da jirgin Boeing Business Jets (BBJ) 737, Gulfstream G550, Gulfstream G500, sai Falcon 7X guda biyu, HS 4000, da Agusta 139 guda biyu, da kuma Agusta 101 shi ma guda biyu.
Kasafin kudin shekarar 2015
Idan za a iya tunawa, a shekarar 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin rage kudaden da za a kashe a gwamnati tare da cewar zai sayar da jiragen sama na alfarma guda biyu da suka hada da Dassault Falcon 7x da kuma Beechcraft Hawker 4000.
Sai dai sayar da jiragen ya zo da matsala, inda mafi akasarin wadanda suka nuna sha'awar sayen jirgin suka ce za su iya biyan dala miliyan 24 ne kawai, amma daga bisani aka dai daita akan dala miliyan 11.
Fagen kasafin kudi kuwa, an samu hawa da sauka a cikin 'yan shekarun nan. Misali, a 2016, an ware Naira Biliyan 3.65 ne don tafiye tafiyen shugaban a jirgin sama, amma daga bisani aka kara kudin a shekarar 2017, 2018 da 2019, zuwa Naira Biliyan 4.37, Naira Biliyan 7.26 da kuma Naira Biliyan 7.30.
Sai dai, kudin sun dan ragu da Naira Miliyan 503.75 a shekarar 2020 lokacin da aka ware Naira Biliyan 6.79 na tafiye tafiyen sakamakon annobar Korona da ta barke, wacce ta kawo tsaiko na tafiye tafiye.
Amma shekaru biyun da suka biyo bayan wannan annoba, kasafin ya haura har zuwa Naira Biliyan 12.55 a shekarar 2021 da kuma Naira Biliyan 12.48 a shekarar 2022.
Ra'ayin mai fashin baki
Da ya ke fashin baki kan wannan dambarwa, shugaban kungiyar mamallakan jiragen sama ta Najeriya, kuma tsohon shugaban kamfanin Associated Airlines, Alex Nwuba, ya ce:
"Muna sane da cewa darajar naira ta fadi da kusan kaso hamsin, komai ya yi tsada da kusan kaso 30, ga kuma rashin aiki da ya kara jawo tabarbarewar tattalin arziki."
"Za mu iya cewa dole a samu karin kudin da za a kashe a tafiye tafiyen shugaban kasar ta jirgin sama. "
Tabbas sufurin jiragen sama wani abu ne da ya zamo kusan wajibi ga kowacce gwamnatin, sai dai a lokaci irin wannan na karancin kudaden shiga da tabarbarewar tattalin arziki, akwai bukatar a nisanta da amfani da kayan gwamnati ba bisa ka'ida ba. Dole a alkinta dukiyar al'umma."
Tafiyar farko da Shugaba Tinubu ya yi zuwa turai
Legit Hausa ta ruwaito maku cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa kasar Faransa bayan kwanaki 23 da hawa kan karagar mulkin kasar.
Shugaban kasar ya halarci wani taro ne a kasar kan tattalin arziki wanda aka gudanar a ranakun 22 da 23 na watan Yunin 2023.
Asali: Legit.ng