Wata sabuwa: FG ta sanya jirgin shugaban ƙasa a kasuwa, za ta sayar da shi

Wata sabuwa: FG ta sanya jirgin shugaban ƙasa a kasuwa, za ta sayar da shi

- Gwamnatin tarayya ta saka daya daga cikin jiragen Shugaban kasa a kasuwa

- Jirgin da za a siya shine Hawker 4000, mai lamba 5N-FGX/: RC 066, an kuma siye shi a shekarar 2011 kan kimanin dala miliyan 22.91

- An bukaci masu ra’ayin siyan jirgin su gabatar da farashinsu cikin mako guda

Rahotanni sun kawo cewa an sanya daya daga cikin jiragen Shugaban kasa, Hawker 4000, mai lamba 5N-FGX/: RC 066 a kasuwa.

Gwamnatin tarayya, a cikin wani talla da ta biya aka yi mata a jaridar kasar, a ranar Laraba, ta sanar da shirinta na siyar da jirgin ga wadanda suka shirya siya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jirgin ya kasance daya daga cikin rundunar jirage 10 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarar a lokacin da ya hau kujerar mulki a 2015.

KU KARANTA KUMA: Na yi alƙawarin COVID-19 ba za ta kashe kowa a Taraba ba - Gwamna Ishaku

A bisa ga bayanai, an siye shi a shekarar 2011 kan kimanin dala miliyan 22.91.

Wata sabuwa: FG ta sanya jirgin shugaban ƙasa a kasuwa, za ta sayar da shi
Wata sabuwa: FG ta sanya jirgin shugaban ƙasa a kasuwa, za ta sayar da shi Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

An tattaro cewa jirgin wanda ke da ikon daukar fasinjoji tara, shine na uku da za a siyar tun bayan da Buhari ya yi umurnin rage yawan rundunar jiragen ta hanyar siyar dasu.

Shugaban kasar ya kuma bayyana halin da tattalin arziki ke ciki a matsayin dalili.

A tallan, an shawarci masu ra’ayin siyan su gabatar da farashinsu ga Shugaban kwamitin siyar da jirage, ofishin mai ba Shugaban kasa shawara a harkar tsaro, ofishin kula da ayyuka na musamman, ofishin babban sakatare gwamnatin tarayya.

“Dan Allah a lura cewa dole a gabatar da dukkanin farashi da za a siya jirgin cikin sati guda da wannan wallafar. Akwai bukatar duba tushe a cikin matakan cinikin. Duk wanda ke son ganin jirgin daga cikin masu siyan za a basu damar yin hakan cikin mako guda daga ranar wannan tallan,” cewar jawabin tallan.

KU KARANTA KUMA: Daga ƙarshe: Buhari ya amince har yanzu Boko Haram da ƴan bindiga na cin kasuwarsu a Nigeria

Da aka tuntube shi don jin karin bayani, babban mai ba Shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu, ya ce bai da wani karin bayani bayan wanda aka gani.

“Yana ciki. Bani da Karin bayani fiye da abunda ke a tallan. Nagode,” in ji shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng