Dakarun Soji Sun Kai Samame Filato da Kaduna, Sun Murkushe 'Yan Bindiga 4 da cafke 'Yan Ta'adda 19
- Hukumar sojin Najeriya ta sanar da gagarumin nasara da dakarunta suka samu a jihohin Filato da Kaduna
- Dakarun sojin sun yi nasarar murkushe yan ta'adda 4 tare da cafke wasu 19 a samamen da suka kai jihohin arewan guda biyu
- Jami'an tsaron sun gudanar da ayyukan ne a ranar 29 ga watan Oktoba zuwa 5 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Dakarun rundunar soji na Operation SAFE HAVEN (OPSH) sun bindige yan bindiga hudu tare da kama wasu mutane 19, ciki harda masu garkuwa da mutane, barayin shanu da masu fashi da makami a samame da suka kai mabuyansu a jihohin Filato da Kaduna.
Kamar yadda rundunar sojin Najeriya ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fita a shafinta na X a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, an kai samamen ne daga 29 ga watan Oktoba zuwa 5 ga watan Nuwamban 2023.
Nasarori da dakarun soji suka samu a Oktoba
A ranar 29 ga watan Oktoba, dakarun sun kama wasu mutum biyu da ake zargin masu fataucin miyagun kwayoyi ne, Minsta Obinna Nwafor da Fatai Lawal a kasuwar Kujiya Bukuru da ke karamar hukumar Jos ta kudu, jihar Filato sannan suka kwato wata bindiga yar gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Washegarin ranar, jami'an sashi na 7 sun kama wani mai garkuwa da mutane, Bawa Ahmad a kauyen Kumuru da ke karamar hukumar Zango Kataf ta jihar Kaduna sannan suka kwato bindiga da harsasai.
Haka kuma, a ranar 30 ga watan Oktoba, dakarun sojin sun kama wasu mutum uku, Ibrahim Mohammed, Salisu Abdullahi da Idris Abdullahi kan harin da aka kai wa manoma a kauyen Mai Hakorin Gold da ke karamar hukumar Bokkos, jihar Filato.
Har wayau, sojoji sun kama wasu mutum uku David Emmanuel, Moses Dalyop da Gabriel Davou da hannu a kisan wani dan achaba, Abdulkarim Saidu, a kauyen Shonong da ke karamar hukumar Riyom, jihar Filato.
Dakarun sojin sun kuma ceto wata mata mai suna Ms Abigail Felix, wacce aka yi garkuwa da ita a ranar 28 ga watan Oktoban 2023, a kauyen Angwan Malam da ke karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna. Tuni aka sada ta da yan uwanta.
Ayyukan sojin a watan Nuwamban 2023
A ranar 1 ga watan Nuwamba, an kama wasu masu kwace babur, Samaila Nasiru da Bashir Sani a yankin Riyom, jihar Filato.
Dakarun sojin da hadin gwiwar yan CJTF sun kuma ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Zobolo da ke karamar hukumar Jos ta arewa, jihar Filato.
Sun kama wani Mista Suleimanu Audu a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba a kauyen Gidan Auta kan garkuwa da yi wa wasu mutum biyu fyade a ranar 24 ga watan Satumba.
A wannan rana, jami'an tsaro sun kuma kama Sarajo Adam, wani kasurgumin dan fashi da makami a kauyen Kwog, a karamar hukumar Barkin Ladoi. An tattaro cewa yana cikin wadanda ake nema ruwa a jallo kan ayyukan fashi da makami a yankin da kewaye.
Ga sanarwar a kasa:
Sojoji sun murkushe yan Boko Haram a Yobe
A wani labarin, mun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun halaka mayakan kungiyar ta'addanci guda biyar tare da kama wani daya a garin Geidam da ke karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe, a daren ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kwato bindigogin AK-47 da dama da babura mallakin yan ta'addan a yayin faruwar lamarin inda sauran yan ta'addan suka tsere da raunuka da suka samu sanadiyar harbi.
Asali: Legit.ng