Barayi Sun Sacewa Najeriya Man Fiye da Naira Tiriliyan 4.3 a Shekaru 5 Inji NEITI
- Gwamnatin tarayya ta yi asarar makudan kudin da ya kamata a ce an samu daga saida danyen mai a kasuwannin Duniya
- A sakamakon masu fasa bututunmai da su ka addabi Najeriya, an sace danyen man fiye da Naira Tiriliyan 4.3 a shekaru biyar
- Daga shekarar 2017 zuwa 2021, barayi sun fasa bututu sun sace ganguna fiye da miliyan 200 na arzikin danyen man Najeriya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce danyen man sama da N4.3tr aka sace a sakamakon fasa bututu da wasu miyagu su ke yi a kasar nan.
Business Day ta kawo rahoto a ranar Litinin cewa a cikin shekaru biyar, an fasa bututu sau 7, 143 an yi awon gaba da man Najeriya.
Shugaban hukumar NEITI na kasa, Ogbonnaya Orji, ya shaida haka da yake gabatar da takardarsa a wajen taro da aka shirya a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi taro a kan satar man Najeriya
A makon nan aka kira babban taro a kan harkar tsaro da fasahar zamani da za a bi domin a kare bututun mai daga masu sace arzikin al’umma.
Ogbonnaya Orji ya ce satar ta zama barazana ga hako mai da ake yi a Najeriya.
Ta bangaren tattalin arziki kuwa, masu wannan danyen aiki su na jawo asara, ba a barin kamfanoni su samu ribar da ya kamata daga man.
Asarar man N4.3tr a shekaru 5
Punch ta ce shugaban na NEITI ya gabatar da alkaluma da za su gaskata abin da yake fada na irin satar da aka yi a tsakanin 2017 zuwa 2021.
A cewar Orji, an yi asarar ganguna miliyan 208.639 wanda da sun shiga kasuwa, za a iya saida su a kan akalla $12.74m ko N4.325tn a yau.
An kashe kudin gyaran bututun mai a banza?
Kungiyar kwararrun masu harkar kula da bututun mai da su ka shirya taron sun ce tattaunawar za ta taimaka a bunkasa tattalin arziki.
Hukumar NEITI ta ce a daidai wannan lokaci kuma an kashe N471.493bn saboda ayi gyara ko kuwa gadin bututun nan da aka rika fasawa.
Israila za ta shigo birnin Abuja?
Kwanakin baya aka ji Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi kaca-kaca da sabon Ministan Abuja, Nyesom Wike a kan tsare-tsarensa.
Amma Cif Femi Fani-Kayode ya yi wa fitaccen malamin musuluncin radd, ya ce a ja-kunnen Dr. Gumi domin kalamansa za su iya jawo rikici.
Asali: Legit.ng