Babban labari: Buhari ya yi wani sabon nadi, ya bada kujerar Shugaban Hukumar NEITI

Babban labari: Buhari ya yi wani sabon nadi, ya bada kujerar Shugaban Hukumar NEITI

- Orji Ogbonnaya Orji shi ne sabon shugaban ma’aikatar NEITI a Najeriya

- Dr. Ogbonnaya Orji ya gaji Waziri Adio, zai bar wannan kujera ne a 2026

- Orji wanda kafin yanzu Darekta ne a NEITI ya taba aiki da UNDP a baya

Muhammadu Buhari ya amince da nadin Orji Ogbonnaya Orji a matsayin sabon shugaban hukumar Nigeria Extractive Industries Transparency Initiative (NEITI).

Shugaban kasa ya nada Dr. Orji Ogbonnaya Orji ne bayan Waziri Adio ya kammala wa’adinsa na tsawon shekaru biyar a jiya ranar Alhamis, 18 ga watan Fubrairu, 2021.

Kafin ya hau wannan kujera, Dr. Orji Ogbonnaya Orji, shi ne darektan sadarwa da wayar da kai na NEITI, hakan na nufin an zakulo sabon shugaban ne daga cikin gida.

A baya Dr. Orji Ogbonnaya Orji ya yi aiki a gidan rediyon Najeriya, sannan ya tafi ma’aikatar NDP ta majalisar dinkin Duniya, daga bisani sai ya dawo hukumar ta NEITI.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya naɗa sababbin shugabanni a NSCDC da NCoS

Kamar yadda aka bayyana a shafin NEITI, sabon shugaban ya na digirgir da digirdigir a fannin siyasar tattalin arziki da kuma ilmin cigaban kasashe a jami’ar nan Abuja.

Ogbonnaya Orji ya shafe fiye da shekaru goma ya na aiki da hukumar kafin ya kai wannan matsayi.

Hukumar NEITI wanda gwamnatin Olusegun Obasanjo ta kafa a cikin shekarar 2003, ita ce mai alhakin sa ido domin ganin an yi gaskiya wajen tafiyar da albarkatun kasar nan.

Da ya shiga ofis, Dr. Ogbonnaya Orji ya yi godiya da shugaba Muhammadu Buhari da ya ba shi wannan mukami, ya yi alkawarin za a kara gyara NEITI a karkashin jagorancinsa.

KU KARANTA: Buhari ya nada sabon shugaban EFCC

Babban labari: Buhari ya yi wani sabon nadi, ya bada kujerar Shugaban Hukumar NEITI
Orji Ogbonnaya Orji @DrOrjiOOrji Hoto: @Nigeriaeiti
Asali: Twitter

Shugaban ya yi alkawari cewa ba da dade wa ba, zai fito da tsare-tsaren da zai bi wajen kai ga nasara.

Kwanaki kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Samuel Adebayo a matsayin sabon babban hafsan leken asirin tsaro na Najeriya (CDI).

Janar Samuel Adebayo zai kuma rike kujerar shugaban hukumar leken asirin tsaro na kasa (DIA).

Sanarwar da aka fitar ta bayyana cewa, Manjo-Janar Samuel Adebayo ya gaji Air Vice Marshal Muhammed Usman (rtd) ne, wanda ya yi ritaya daga aiki kwanan nan.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel