Yan Sanda Sun Cafke 'Yan Fashi 4 Kan Zargin Hallaka Dan Uwansu Saboda Yi Mu Su Baba-kere da Ganima
- Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar kama wasu 'yan fashi da zargin hallaka dan uwansu kan ganimar fashi da su ka samu a jihar Ondo
- Kakakin rundunar a jihar, Funmilayo Odunlami ta ce sun kama mutanen hudu kan zargin kisan a Ondo a jiya Litinin 6 ga watan Nuwamba
- Ta ce jami'ansu sun cafke Blessing Okon wanda ya jagoranci rundunar zuwa kamo sauran mutanen hudu kan zargin kisan da su ka aikata
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Rundunar 'yan sanda sun cafke gungun 'yan fashi guda hudu kan zargin kisa a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya.
Rundunar na zargin 'yan fashin ne da hallaka daya daga cikinsu kan rabon kayan ganima da su ka sato, cewar Premium Times.
Mene 'yan sanda su ke zargin 'yan fashin?
Kakakin rundunar a jihar, Funmilayo Odunlami ita ta tabbatar da haka a jiya Litinin 6 ga watan Nuwamba a Akure babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta bayyana haka ne yayin gurfanar da 'yan fashin da kuma wasu 15 wadanda ake zargi da aikata laifuka da dama.
Funmilayo ta ce an kama Blessing Okon kan zargin kisan inda ya jagoranci kama sauran mutanen uku, cewar TheCable.
Mene dalilin hallaka dan uwan nasu?
Daga cikin wadanda aka kaman akwai Gabriel Japhet da Osha Phenus da kuma Gbenga Timothy.
Ta ce Okon ya tabbatar da cewa sun yi ajalin Mista Jadi ne saboda ya hana su kasonsu na fashi da su ka aikwatar a jihar.
Daga cikin wadanda aka gurfanar a gaban ofishin 'yan sanda sun hada da ma su aikata laifuka da su ka hada da mallakar makamai da alaka da kungiyoyin asiri.
NSCDC ta cafke mata kan damfarar gidan marayu
A wani labarin, Hukumar tsaro ta NSCDC ta yi nasarar cafke wata mata da zargin damfarar gidan marayu naira miliyan daya.
Matar mai suna Folasade 'yar shekaru 38 ana zarginta da karbar makudan kudade a hannun mutane da sunan gidan marayun.
Yayin bincike, rundunar ta gano matar ta shafe watanni tara ta na wannan badakala da baba-kere da kayan marayu.
Asali: Legit.ng