An kama wani Fasto a Legas kanyin gidan marayu

An kama wani Fasto a Legas kanyin gidan marayu

- An damke wani fasto da ya bude gidan marayu a gidan shi dake jahar Legas ba kan ka'ida

- Faston da aka bayyana a matsayin Onoyngu Chubuike, wanda ya asassa Voice Salvation Charitable Organisation a jahar Legas, an kama shi kan yin gidan marayu a gidan shi ba tare da bin doka ba

An kama wani Fasto a Legas kanyin gidan marayu

Kamar yadda jaridar the Nation ta wallafa, an gano cewa gidan marayun da aka bude a shekara 2010 , amma ba'a yanka mai rejista ba ta dokar jahar Legas .

Bayan wani yaro ya fara ciwo, an nemi faston da ya bada labarin abunda ya faru inda ya kasa samar da bayanin.

Sai dai faston ya tabbatar da cewa ya samu lasisin bude gurin daga hukumar Co-ooerate Affairs , bayan haka ya samu goyon bayan na bude gurin a shekara 2010 dan taimakon yaran da suka rasa iyayen su.

Kungiyar sa ka ta jahar Legas da ma'aikatar yara da matasa suka auka gidan shi dake unguwar Ojo jahar Legas inda suka samu yaran.

KU KARANTA: Hukumar ‘yan sanda ta saki sunayen wadanda sukayi nasarar samun aiki.

A lokacin da yake magana yace" ni asalin dan Anambra ne, ubangiji ya umurce ni da in yi wannan aiki ga masu dan karfi kamar zawarawa, yaran da basu da iyaye, da mutanen da basu da gida, na tanada kulawa mai kyau ga wadannan yaran har iyayen su su samu halin daukar nauyin su, wadan nan da aka bari zan iya daukar nauyin su har jami'a.

Yace wasu daga cikin yaran yan sanda suka kawo man su, wasu kuma iyayen su suka kawo man su an haifi su ba tare da aure ba, kuma basu da abun daukar nauyin su.

Lokacin da ake magana kan lamarin kwamishinan matasa da masana'an tu, yace za'a dauki mataki akan faston , in ka bude gidan marayu a jahar Legas kayi laifi, rijistar da kayi da Co-operate Affairs ba zata baka damar bude gidan marayu ba.

Gidan marayu ba kungiya bace ta taimako da kake cewa ubangiji ya umurce ka ka bude.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng