Sarkin Legas Ya Bai Wa Tinubu, Atiku da Peter Obi Muhimmin Shawara Bayan Hukuncin Kotun koli

Sarkin Legas Ya Bai Wa Tinubu, Atiku da Peter Obi Muhimmin Shawara Bayan Hukuncin Kotun koli

  • An bukataci Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, da su yi mai yiyuwa domin ganin Najeriya ta samu ci gaba a gwamnatin jam'iyyar APC
  • Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, ya bukaci Atiku da Obi, su hada kai da shugaban kasa Bola Tinubu, domin ganin an kai Najeriya tudun mun-tsira
  • Yayin da ya ke nuna irin kalubalan da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, Sarkin ya bukaci 'yan siyasar da su ajiye adawa a gefe su fuskanci matsalolin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ikeja, Legas - Sarkin Legas (Oba of Lagos), Riliwan Akiolu, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da abokan hamayyarsa a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar, Peter Obi, da dai sauransu, da su hada kai wajen ganin Nijeriya ta ci gaba.

Kara karanta wannan

Jirgin ruwan N5.5bn: Abin da ’yan Najeriya suka shuka ake girba – Tsohon dan takarar shugaban kasa

Oba Akiolu, wanda ya zanta da wakilin jaridar The Punch a Burtaniya (UK), ya ce ya kamata 'yan siyasa su fi mayar da hankali kan ci gaba da walwalar al'umma.

Atiku, Tinubu da Obi
Sarkin Legas, ya jaddada bukatar Shugaba Tinunu, Atiku da Obisu su hada kai don ci gaban Najeriya Hoto: Atiku Abubakar / Bola Ahmed Tinubu / Peter Obi
Asali: Facebook

A cewar sa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abubuwa da dama na faruwa a kasarmu. Yan siyasa ba sa fada, za su zo su shirya nan gaba. Ya kamata kowannensu yazo su hada kai su ciyar da kasar Najeriya gaba. Akwai rashin ayyukan yi, mu magance wannan matsalar."
"Rashin tarbiyar rayuwa da son zuciya shi ne matsalarmu. Mun yi nisa daga tafarkin ubangiji. Duk mutumin da ya kasance mai dattako ne, ubangiji zai saka masa."

Ko da aka tambaye shi ko yana nufin Tinubu, Atiku da Obi su zo su hada kai, sai cewa ya yi:

Ya kamata su zo su hada kai domin ci gaban Najeriya. Shugabanci daga Allah ne. Shugaban yanzu, na taba fada masa cewa akwai dalilin da ya sa Allah ya basa mulkin. Amma duk wanda ke kan irin wannan matsayin sai ya hada da addu'a, ya zama mai gaskiya da kuma yin abubuwan da ba ayi zato ba.

Kara karanta wannan

“Ina alfahari matuka”: Tinubu ya caccaki Atiku da Obi yayin da yake jawabi ga ministocinsa

Kotu ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaben shugaban kasar 2023

Legit ta ruwaito maku cewa kotun koli a watan Oktoba ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabreru, 2023.

Kotun kolin ta tabbatar da hukuncin da kotun zabe ta yanke, wanda ya yi watsi da korafin da Atiku da Obi suka gabatar na kalubalantar nasarar Tinubu

Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori

A wani labarin makamancin wannan, jaridar Legit Hausa ta ruwaito yadda Shugaba Bola Tinubu ya yi karin haske a kan babatun da aka ji ya yi kwanakin baya.

Daily Trust ta rahoto Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar litinin, 20 ga watan yuni 2022, yana cewa ya yi hakan ne saboda ya lura ana neman yi masa kafa.

Kara karanta wannan

‘'Gwamnatin Tinubu za ta tsamo 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci,’' Betta Edu

Da yake jawabi a fadar Mai Martaba Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, an ji Tinubu yana bayanin fito da abin da ya birne na tsawon shekaru a cikin zuciyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.