Shahararren Lauya Ya Fada Wa Atiku da Obi Abin da Za Su Yi Bayan Hukuncin Kotun Koli
- Shahararren lauya, Inibehe Effiong, ya fada wa Atiku Abubakar da Peter Obi abin da za su yi bayan hukuncin kotun koli na tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu
- Effiong ya ce ya kamata Atiku da Obi su fara gudanar da aikin adawa ta hanyar bin diddigin ayyukan gwamnatin Tinubu
- A zantawarsa da jaridar Legit, ya ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ba ta cika alkawuran da ta dauka a zabukan da suka gabata ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Legas - Shahararrren lauyan kare hakkin bil Adama, Inibehe Effiong ya magantu kan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023 da ya gabata.
Effiong ya ce yana fatan majalisar tarayyar Najeriya ta sake fasalin dokar zabe domin fayyace matsayin shari'a, musamman akan abinda ya shafi sanar da sakamakon zabe ta hanyar saka wa a shafin yanar gizo.
Ya jaddada cewa sashe na 60 da kuma sashe 65 na kundin dokar zabe da kuma sakin layi na 38 na dokokin gudanarwar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), sanar da sakamakon zabe kai tsaye a shafin hukumar na yanar gizo wajibi ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata zantawa da jaridar Legit, sanannen lauyan ya ce INEC ba ta gudanar da zabukan shekarar 2023 yadda ya kamata ba, sakamakon gaza cika wasu alkawura da ta dauka.
"Hukumar zabe ta karya alkawarin da ta daukar wa 'yan Nigeria, don haka hukuncin da kotu ta yanke bai wanke hukumar ba, illa ma fito da laifin hukumar karara ya yi saboda ko shi alkalin kotun koli, Mai Shari'a Okoro, a hukuncinsa ya fadi cewa rashin sanya sakamakon zaben kai tsaye a yanar gizo ya kawo nakasu ga zaben gaba daya."
Ya kamata shugaban hukumar INEC ya yi murabus - Effiong
Effiong ya ce abinda Farfesa Yakub Mahmood ya yi a zaben da ya gabata abin kunya ne, na sanar da cewa hukumar za ta sanya sakamakon zaben kai tsaye a yanar gizo kuma har aka ware kudade domin tabbatar da hakan, amma a karshe bai cika alkawarin da ya dauka ba.
Ya ce ya kamata shugaban hukumar INEC ya yi murabus daga kujerarsa akan rashin cika alkawari.
Da ya ke jawabi akan Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar LP, Effiong ya ce akwai bukatar yan takarar biyu su mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan adawa na bin diddigin ayyukan gwamnatin Shugaba Tinubu.
"Yanzu aikin adawa zai fara, wanda shi ne bin diddigin munanan ayyukan gwamnati da shugaban kasa, tare da kama shi da alhakin duk abinda ya faru ba dai dai ba. Sannan su tabbatar sun taka rawar da ta dace na ganin an gina kasar."
A cewar sanannen lauyan.
Effiong ya ce ya goyi bayan kotun koli na yin watsi da sabuwar hujjar da Atiku ya gabatar akan Tinubu, saboda wa'adin duba hujjojin karar zabe kwana dari da tamanin ne, don haka akwai bukatar wa'adin ya yi aiki akan kararrakin zaben shugaban kasa.
Shugaba Tinubu ya caccaki Atiku da Obi bayan samun nasara a kotu
Jaridar Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya caccaki Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na jam'iyyar LP bayan ya nasarar da ya samu a doguwar shari'ar da suka yi da shi a kotun koli.
Da yake jawabi ga Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja da sauran mambobin majalisarsa a wani bidiyo da Legit Hausa ta gano, shugaban kasar ya ce yana alfahari da kayar da Atiku da Obi da ya yi a zabe da kotu.
Asali: Legit.ng