Dakarun Sojoji Sun Halaka Ƴan Bindiga Masu Yawa a Zamfara Yayin Dakile Wani Kazamin Hari
- Dakarun sojoji na atisayen 'Operation Hadarin Daji' sun samu nasarar daƙile wani kwanton ɓauna da miyagun ƴan bindiga suka yi musu a jihar Zamfara
- Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar daƙile wani farmaki da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Karazau cikin ƙaramar hukumar Bungudu
- A yayin fafatawar ƙwararrun dakarun sojojin sun samu nasarar fatattakar ƴan bindigan tare da halaka masu daga cikinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na atisayen 'Operation Hadarin Daji' a jihar Zamfara, sun samu nasarar daƙile wani kwanton ɓaunan ƴan bindiga, sannan suka halaka masu yawa daga cikinsu.
Sojojin sun kuma daƙile harin da ƴan ta'adda suka kai ƙauyen Karazau da ke ƙarƙashin gundumar Kwatarkwashi a ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara da sanyin safiyar ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Channels tv.
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘Operation Hadarin Daji', Kyaftin Yahaya Ibrahim ya fitar a ranar Lahadi, yace sojojin sun kai ɗauki bayan sun samu kiran gaggawa cewa ƴan ta'addan sun kai hari a ƙauyen Karazau da ke gundumar Kwatarkwashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojojin suka fatattaki ƴan bindigan
Ya ce a lokacin da sojojin suka tunkari ƙauyen, ƴan ta'addan ɗauke da makamai sun yi wa sojojin kwanton ɓauna.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Duk da haka, sojojin da ke cikin shirin fafatawa waɗanda ke da juriya tare da dabarun yaƙi, sun kawar da kwanton ɓaunan tare da tilasta wa ƴan ta'addan guduwa yayin da, da yawa daga cikinsu suka haɗu da ajalinsu."
"Daga baya, sojojin sun mamaye yankin gaba ɗaya tare da yin sintiri cike da ƙarfin gwiwa domin hana ƴan ta'addan samun sukuni."
Dakarun Sojoji Sun Halaka Ƴan Bindiga
A wani labarin kuma, dakarun sojoji a jihar Zamfara sun samu nasarar halaka wasu miyagun ƴan bindiga mutum 10, tare da ceto wasu mutum tara a wata fafatawa da suka yi.
Dakarun sojojin sun yi arangama da ƴan bindigan ne a ƙauyen Danmarke bayan sun samu bayanan sirri kan motsin su.
Asali: Legit.ng