Lokaci Ya Yi: Yadda Wata Mata Ta Rasa Ranta Ana Tsaka da Ibada a Jihar Ogun
- An shiga jimami a jihar Ogun bayan wata mata ta faɗi ana tsaka da ibada a coci sannan ta rasa ranta daga baya
- Matar mai shekara 75 a duniya ta faɗi ne a cocin Mountain of Fire and Miracles Minitries ta yankin Ibafo da ke jihar Ogun
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da cewa matar ta rasu daga baya bayan an kai ta wani asibiti a Sagamu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Ogun - Wata mata mai suna Bisi Adewumi ta cocin Mountain of Fire and Miracles Ministries ta faɗi ana tsaka da gudanar da addu'a a ɗakin taro na cocin da ke yankin Ibafo a jihar Ogun.
Matar wacce rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta bayyana a matsayin ƴar shekara 75, ta rasa ranta daga baya lokacin da ake duba lafiyarta a wani asibitin gwamnati da ke Sagamu.
Rundunar ƴan sandan ta ce Fasto Ekikere Esiere ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda da ke Ibafo a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda marigayiyar ta rasa ranta
Rundunar ta bayyana cewa Esiere ya yi iƙirarin cewa an garzaya da marigayiyar zuwa asibitin cocin domin kula da lafiyarta bayan ta faɗi da misalin karfe 5:30 na yamma a ranar Alhamis.
Daga bisani, an ce an garzaya da marigayiyar babban asibitin Sagamu, inda aka ce ta rasu ne a ranar Juma’a, rahoton shafin Tori ys tabbatar.
A halin da ake ciki, a wata zantawa da jaridar Punch a ranar Asabar, 4 ga watan Nuwamba, jami’ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar, Omolola Odutola, ta ce an ajiye gawar a daƙin ajiye gawa na asibitin.
"Har yanzu dai babu wani ɗan uwan mamaciyar da ya zo ɗaukar gawar. Marigayiyar ana tunanin ta kai shekara 75 a duniya. A halin yanzu, ana cigaba da gudanar da bincike." A cewarta.
Malamin Coci Ya Mutu a Benue
A wani labarin kuma, babban malamin cocin St. Joseph Catholic da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benuwai, Rabaran Faustinus Gundu, ya riga mu gidan gaskiya.
Babban faston dai ya yi bankwana da duniya ne bayan tsawa ta faɗo masa lokacin da ake yin ruwan sama.
Asali: Legit.ng