Ministan Tinubu da Hatsarin Jirgin Sama Ya Rutsa da Shi Ya Magantu, Ya Faɗi Halin da Yake Ciki

Ministan Tinubu da Hatsarin Jirgin Sama Ya Rutsa da Shi Ya Magantu, Ya Faɗi Halin da Yake Ciki

  • Ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabi, ya bayyana halin da yake ciki bayan hatsarin jirgin sama ya ritsa da shi a Ibadan
  • Adelabi ya ce babu wani abun damuwa da ɗaga hankali domin yana cikin ƙoshin lafiya babu abinda ya same shi
  • A jiya Jumu'a ne Jirgin saman da ya taso daga Abuja ya gamu tangarɗa yayin sauka a filin jirgi, inda ya sauka mita 50 nesa da titinsa

A ranar Asabar, 4 ga watan Nuwamba, Ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabi, ya kawar da duk wata fargaba da ake yi kan lafiyarsa bayan hatsarin jirgin sama da ya ritsa da shi a ranar Juma'a.

Wata majiya ta kusa da ministan ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Ibadan cewa Adelabu na cikin koshin lafiya kuma bai damu da lamarin ba.

Kara karanta wannan

FG ta yi karin bayani, ta fara bincike yayin da jirgin sama dauke da ministan Tinubu ya yi hatsari

Adelabu ya ce yana cikin koshin lafiya
“Ina Cikin Koshin Lafiya”, Ministan Tinubu da Ya Yi Hatsarin Jirgin Sama Ya Magantu Hoto: Adebayo Adelubu
Asali: Facebook

An rahoto cewa jirgin sama mai zaman kansa da ke dauke da ministan da wasu hadimansa ya yi hatsari a kusa da filin jirgin saman a yammacin ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba.

"Ministan yana ganin lamarin ba abu ne da za a damu da shi ba. A zahirin gaskiya ba abu mai tsanani bane, kuma cewa haka ya dauki abun," cewar wani hadimin ministan da ya nemi a sakaya sunansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gaba daya fasinjojin jirgin na cikin koshin lafiya

Hadimin ya bayyana cewa babu ko mutum daya daga cikin fasinjojin da ya samu rauni, rahoton The Nation.

"Duk wani da ke cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru ya fita ba tare da wata matsala ba, kuma ba mu da wani dalili na damuwa," in ji hadimin nasa.

Jirgin dai ya taso ne daga Abuja don zuwa Ibadan, amma sai ya sauka mita 50 da inda ya dace sannan ya kutsa cikin wani rami da ke kusa da titin jirgin.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

Hukumar NSIB ta kaddamar da bincike

A halin da ake ciki, hukumar Bincike ta Najeriya (NSIB) ta ce ta fara bincike kan hatsarin jirgin sama mai zaman kansa da ya afku a filin jirgin sama na Ibadan a raeen ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba.

An rahoto cewa a safiyar ranar Asabar, 4 ga watan Nuwamba, jami'an hukumar sun tabbatar da cewar jirgin ya fado, amma ba a rasa rai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng