Tsaro: Amurka Ta Gargadi Yan Kasarta da Su Guji Manyan Otel a Najeriya
- Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya nuna fargaba kan yiwuwar tabarbarewar tsaro a kwanaki masu zuwa
- Wannan sanarwar na kunshe ne a bayanin shawarari da ofishin jakadancin Amurka ya fitar a ranar Juma'a, 3 ga Nuwamba
- An gargadi Amurkawa a Najeriya da su nisanci ottel-otel a garuruwan wasu manyan biranen kasar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Amurka ta yi gagarumin gargadi ga yan kasarta da ke Najeriya, inda ta sanar da su "gagarumin barazana" da ke tattare da wasu manyan otel-otel a manyan biranen kasar.
An saki wannan gargadi ne a matsayin karin bayani na gaggawa ga yan kasar Amurka a ranar Juma'a, 3 ga Nuwamba.
Sanarwar ta bayyana cewa hukumomin tsaron Najeriya suna tsaye kan lamarin domin dakile barazanar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukaci yan kasar Amurka da su yi taka-tsan-tsan a lokacin da suka yi masauki a manyan otel-otel, su kula da muhallinsu, su zamo masu kankan da kai, sannan su yi bitar shawarar tafiye-tafiye a Najeriya kafin zabar masaukinsu.
Sanarwar ya zo kamar haka:
"Gwamnatin Amurka na sane da sahihan bayanai da ke nuna cewa akwai babbar barazana ga manyan otel-otel a manyan biranen Najeriya.
“Hukumomin tsaron Najeriya na aiki tukuru domin dakile wannan barazana.
"Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shawarci yan Amurka da su yi la'akari da wannan bayanin yayin da suke shirin yin masauki ko ziyartar manyan otel-otel a Najeriya."
Sanarwar na kuma dauke da bayanan yadda za a tuntubi ofishin jakadancin Amurka a Abuja da ofishin jakadancin na Lagas koda wani dan Amurka zai bukaci taimako.
Amurka ta gargadi yan kasarta a Najeriya
A wani labarin, mun kawo a baya cewa gwamnatin Amurka ta gargadi al'ummar kasar da su kaucewa zuwa wasu yankunan Najeriya saboda laifukan da suka shafi ayyukan ta’addanci, tashe tashen hankula da garkuwa da mutane.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Amurka ta yi gargadin ne a cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar kan shawarwarin tafiye-tafiye.
Asali: Legit.ng