Harin Boko Haram: Jerin Kasashen Duniya 6 Da Suka Gargadi Yan Kasarsu Mazauna Najeriya Su Kiyayi Abuja

Harin Boko Haram: Jerin Kasashen Duniya 6 Da Suka Gargadi Yan Kasarsu Mazauna Najeriya Su Kiyayi Abuja

Ofishohin jakadancin manyan kasashe a duniya sun fitar da gargadin yiwuwar kai harin ta'addanci birnin tarayya Najeriya Abuja.

A ranar Lahadi, wani sabon rahoto daga ofishin jakadancin Amurka ya bayyana yadda ta bada shawarwari ga yan kasarta mazauna Najeriya su kiyayi Abuja.

Gwamnatin Amurka ta bukaci iyalan ma'akatansu dake zama a Abuja su bar birnin da gaggawa.

Wannan na kunshe cikin sabon shawaran da ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya fitar.

A ranar Litinin, gwamnatin kasar Birtaniya ta fitar da irin wannan gargadi duk dai a kan Abuja.

Biden Sunak
Harin Boko Haram: Jerin Kasashen Duniya 9 Da Suka Gargadi Yan Kasarsu Mazauna Najeriya Su Kiyayi Abuja Hoto: @POTUS, @RishiSunak
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit Hausa ta tattaro muku jerin kasashen da sukayi irin wannan gargadi kawo yanzu:

Kara karanta wannan

Barazanar Tsaro: An Gano Asalin Dalilin Rudewa Amurkawa a Abuja

1. Amurka

2. Birtaniya

3. Jamus

4. Bulgariya

5. Ireland

6. Denmark

Amurka Ta Shawarci Ma'aikatan Ofishinta Su Kwashe Iyalansu Daga Abuja Yanzu

Yayinda ake barazanar harin yan ta'addan a birnin tarayya Abuja, Gwamnatin Amurka ta bukaci iyalan ma'akatansu dake zama a Abuja su bar birnin da gaggawa.

Wannan na kunshe cikin sabon shawaran da ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya fitar.

Wannan ya biyo bayan jawabin Amurka na cewa shirya take da ta fara kwashe yan kasarta dake Najeriya.

A cewar jawabin:

"Mun yi karin bayani kan lamarin barazanar hari a Abuja. Muna baiwa yan kasar Amurka kada suyi tafiya Abuja yanzu."
"Hakazalika ranar 27 ga Oktoba, 2022, an umurci iyalan ma'aikata gwamnatin Amurka dake Abuja su fita daga Abuja saboda tsoron hari."
"Yan Amurka su nemi motar haya su fita daga Abuja. Wadanda basu samu motar haya ba su tuntubi ofishin jakadancin Amurka dake Legas don taimako."

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Kuyi Watsi Da Maganar Amurka, Najeriya Tafi Zaman Lafiya Yanzu: Lai Mohammed

Shi kuwa Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa Najeriya ta fi zaman lafiya yanzu fiye da kowani lokaci a shekarun baya-bayan nan.

Lai ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi a taron UNESCO da ya gudana a birnin tarayya Abuja ranar Talata, rahoton TheCable.

Ya yi martani ne game da gargadin da gwamnatin Amurka da Birtaniya tayi na cewa da yiwuwan yan bindiga su kai hari birnin tarayya Abuja.

Ya tuhumci yan jarida da zuzuta lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel