Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Bankado Masana’antar Kera Makamai a Jihar Arewa, Sun Cafke Mutum 2
- Sojojin Najeriya sun yi nasarar bankado wani katafaren masana’antar kera makamai a jihar Plateau a yau Asabar
- Rundunar sojin ta samu wannan nasara ce bayan samun bayanan sirri a Vom da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar
- Rundunar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Twitter a yau Asabar 4 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau – Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar bankado wani masana’anta da ake kera makamai a jihar Plateau.
Rundunar ta ‘Operation Safe Haven’ ta gano masana’antar ce a Vom da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar.
Mene rundunar sojin ta bankado a Plateau?
Sojin sun yi nasarar bankado kamfanin ne bayan samun bayanan sirri wanda hakan ya sanya kwato muggan makamai daga kamfanin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na Twitter a yau Asabar 4 ga watan Nuwamba.
Ta ce ana kera makaman ne a wurin tare da siyar da su zuwa sauran jihohi wanda ke kara rikicin jihar da kuma Kaduna ta Kudu.
Wasu irin makamai rundunar ta kwato a Plateau?
Daga cikin muggan makaman da aka samu a wurin akwai AK-47 guda 7 da bindigu ma su sarrafa kansu guda 4 da kananan bindigu guda 14.
Sauran sun hada da na’urorin sarrafa karafa da maballar AK-47 guda 11 da kayan da ake sarrafa AK-47 guda 47 da sauran muggan kayan kera makamai.
Har ila yau, daga cikin wadanda ke gudanar da wannan ayyuka da aka cafke akwai Michael Dung mai shekaru 33 da kuma Yusuf Pam mai shekaru 43, cewar The Guardian.
Sojoji sun yi nasarar dakile harin Boko Haram a Kano
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya da hadin gwiwar hukumar DSS sun yi nasarar dakile wani mummunan harin Boko Haram a jihar Kano.
Rundunar ta sanar da cewa ta samu nasarar ce bayan kama wasu mutane biyu da muggan makamai a karamar hukumar Gezawa da ke jihar.
Asali: Legit.ng