Jerin Sunaye: Najeriya, Isra'ila Da Sauran Kasashen Da Amurka Ba Ta Da Jakadu Da Kuma Dalili
- Amurka ta tabbatar da cewa akwai kasashe akalla 31 a fadin duniya da ba ta tura jakadunta ba, cikin su har da Najeriya, Masar, Isra'ila
- Matthew Miller, kakakin ma'aikatar harkokin kasashen waje na Amurka, ya sanar da hakan yana mai cewa har yanzu Amurka ba ta tantance wadanda za ta tura ba
- Miller ya fadi hakan a kan gabar tallafin da Amurka ke ba Isra'ila, kasar da ke ci gaba da harba ababen fashewa a Gaza tun bayan harin Hamas na farko a ranar 7 ga watan Oktoba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Gwamnatin kasar Amurka ta ce har yanzu ba ta da jakada a Najeriya, duk da irin ci gaban da aka samu na kawance a tsakanin kasashen biyu.
Matthew Miller, mai magana da yawun ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje na Amurka, da ke aiki karkashin sakataren Amurka na US 71s, Anthony Blinken, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na X (tsohuwar Twitter).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Miller, Amurka ba ta tura da jakadanta zuwa kasar Najeriya da wasu kasashe 30 ba, sakamakon jiran da ake yi majalisar dattijai ta kasar ta tantance sunayen wadanda aka gabatar mata domin zama jakadu.
Kasashe 31 da kasar Amurka ba ta tura jakadunta ba
Idan aka cire Najeriya, sauran kasashen da Amurka ba da ta jakada a ciki sun hada da:
- Lebanon
- Isra'ila
- Masar
- Azerbaijan
- Lithuania
- Haiti
- African Union
- Turkmenistan
- Albaniya
- Zimbabwe
- Barbados
- Peru
- Ecuador
- Cape Verde
- Laos
- Nijar
- Djibouti
- Malaysia
- Gabon
- Burundi
- Croatia
- Guatemala
- Laberiya
- Somaliya
- Bahamas
- Colombia
- Kambodiya
- Montenegro
- Timor-Leste
- Tsibirin Marshall
Karanta maganar ta sa:
Alakar da ke tsakanin Isra'ila da Amurka
Rahotanni sun bayyana cewa Amurka na goyon bayan Isra'ila akan ruwan ababen fashewa da ta ke saukar wa garuruwan Zirin Gaza, tun bayan da Hamas ta kaddamar da hari kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
Babban Malami Joshua Iginla, shugaba kuma wanda ya assasa majami'ar Champions Royal Assembly, ya bukaci shuwagabannin kasashen duniya da su kawo karshen wannan fada da ake yi tsakanin Isra'ila da Gaza, gudun kar ya koma yakin duniya na uku.
A cikin wani bidiyo da majami'ar ta wallafa a shafinta na YouTube, malamin ya ce ya hango "wani babban yaki da ke tunkaro duniya. Kamar wata annoba, ba wai ta cutar rashin lafiya ba, sai dai annoba ta bindigu"
Tsakanin Isra'ila da Falasdinu: "Netanyahu na son haddasa yakin duniya na uku", cewar tsohon minista
Jaridar Legit Hausa ta ruwaito maku cewa Farfesa Bolaji Akinyemi, tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, ya yi zargin cewa Benjamin Netanyahu, firaministan ƙasar Isra’ila, yana yunkurin kawo yaƙin duniya na uku.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, tsohon ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na ARISE a ranar Talata 10 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng