An Waiwayi Mutanen da Yan Bindiga Suka Addaba a Zamfara, Gwamna Ya Karɓo Musu Agaji Mai Tsoka

An Waiwayi Mutanen da Yan Bindiga Suka Addaba a Zamfara, Gwamna Ya Karɓo Musu Agaji Mai Tsoka

  • Gwamnan Zamfara ya karɓo kayan agajin gaggawa na al'ummar jihar Zamfara waɗan da lamarin yan bindiga ya shafa
  • Dauda Lawal ya karɓi kayayyakin ne yayin da ya kai ziyara ga hukumar kula da ƴan gudun hijira da bakin haure ta ƙasa a Abuja
  • Ya kuma roƙi hukumar da ta bai wa jihar Zamfara fifiko duba da yadda matsalar tsaro ta yi wa jihar katutu

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karbi kayan agajin gaggawa na wadanda hare-haren ƴan bindigan daji ya shafa a jihar.

Gwamnan Dauda Lawal da kwamishinan hukumar ƴan gudun hijira.
Gwamna Lawal Ya Karbi Tallafin Gaggawa Na mutanen da lamarin Yan Bindiga ya shafa Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Lawal ya karbi kayayyakin ne ranar Alhamis yayin da ya ziyarci hedikwatar hukumar kula da ‘yan gudun hijira, da bakin haure ta ƙasa da ke Abuja, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun mutu yayin da sojoji suka kai samame wasu yankuna a jihar Kaduna

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar Jumu'a, 3 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya bayyana cewa wannan ziyara da gwamnan ya kai wa hukumar ta zo a lokacin da ya kamata, duba da rawar da hukumar ta gwamnatin tarayya ke taka wa.

A cewarsa, hukumar na taka rawar gani wajen bada agajin gaggawa da waɗan da wani bala'i ko ibtila'i ya afka mawa a ƙasar nan.

Ya samu tarba daga Tijjani Aliyu Ahmed, kwamishinan tarayya na hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure ta gwamnatin Najeriya a Abuja.

Menene maƙasudin wannan ziyara?

A sanarwan da Idris ya fitar, ya ce:

“Makasudin ziyarar Gwamna Lawal ga hukumar kula da ‘yan gudun hijira da baƙin haure ta ƙasa shi ne duba ƙarin hanyoyin da za a taimaka wa waɗanda lamarin ƴan bindiga ya shafa a Jihar Zamfara."

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

"A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya roki Hukumar da ta baiwa Zamfara fifiko saboda matsalar rashin tsaro da kuma tsananin bukatar agaji da mutanen jihar ke ciki."
“Ya bukaci mai girma kwamishinan ya duba batun fadada garuruwan tsugunar da ‘yan gudun hijira da aka gina a Gusau zuwa sauran shiyyoyin jihar."

Bugu da kari, saboda karancin kayan aiki, gwamnan ya jaddada bukatar hadin gwiwa wajen rage radadin ’yan gudun hijira sama da 2000 a Zamfara.

Sarkin Musulmi ya yi magana kan gayyato Zakir Naik

A wani rahoton kuma Sarkin Musulmai ya maida martani ga masu sukar ziyarar da Dakta Zakir Naik ya kawo Najeriya tare da ɗansa.

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce Musulmai na da damar da zasu gayyato ɗan uwansu Musulmi domin wata muhadara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262