An Bukaci Jami'an Tsaro Su Cafke Lauyoyi Da 'Barayin' Man Fetur Da Ke Yekuwar Batanci Ga NNPCL

An Bukaci Jami'an Tsaro Su Cafke Lauyoyi Da 'Barayin' Man Fetur Da Ke Yekuwar Batanci Ga NNPCL

  • Kungiyar NAM ta yi kaca-kaca da hadakar Kungiyar Ma'aikatan Shari'a ta Najeriya kan neman a tsige Mele Kyari, shugaban NNPC daga mukaminsa
  • NAM ta ce ta gano wasu tsiraru cikin ma'aikatan NNPCL ne da suka yi murabus ke hada kai da lauyoyin domin ganin sun yi zagon kasa bisa sauye-sauyen da Kyari da mataimakinsa, Ajiya suke kawo don inganta kamfanin
  • A cewar NAM, tsirarun mutanen da ke neman ganin an tsige Kyari da Ajiya suna fargabar tona asirin haramtattun matatun man fetur da NNPC ke ganowa ne karkashin jagorancin shugaban mai ci a yanzu
  • Kungiyar ta NAM bai wa hadakar lauyoyin wa'adin awa 48 sun fada wa yan Najeriya wani tsari Kyari da Ajani suka kawo wanda ba inganta tattalin arzikin Najeriya zai yi ba, idan ba haka ba su rufe bakinsu

Kara karanta wannan

‘'Gwamnatin Tinubu za ta tsamo 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci,’' Betta Edu

Wata kungiya mai suna Nigeria Accountability Monitors (NAM), ta soki Kungiyar Ma'aikatar Shari'a na Najeriya kan cewa sun bukaci a sauke shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari daga mukaminsa.

Hakazalika, NAM, ta ce ta gano cewa wasu ƙalilan na ma’aikatan kamfanin NNPC da suka yi ritaya, sun hada kai da lauyoyin da ba su da aikin yi, suna cewa wai a sauke Shugaban NNPC Mele Kyari daga mukaminsa.

An soki kungiyar lauyoyi masu son tsige Mele Kyari
Kungiyar NAM ta yi ikirarin tsaffin ma'aikatan NNPCL ne suka hada baki da bara-gulbin lauyoyi don neman tsige Kyari. Hoto: NNPCL
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ita dai ƙungiyar ta NAM ta bukaci daukar matakan tsaro na gaggawa ne don ya zama izna ga lauyoyi masu aiki tare da wadanda ta kira maciya amanar kasa da aka yi wa ritaya daga hukumar ta NNPC, rahoton Vanguard.

Wata sanarwar manema labarai da shugaban ƙungiyar, Sabiu Ibrahim ya sanyawa hannu a yammacin ranar Alhamis, ta bayyana ƙungiyar lauyoyin, ƙarkashin jagorancin wani Adesina Bernard, a matsayin “masu ɓarna ne da ke rawa da bazar wasu tsiraru daga cikin jami’an NNPC da suka yi ritaya kwanan nan, biyo bayan wani aikin gyaran fuska da ake son yi na canza fasalin kamfanin".

Kara karanta wannan

Cin zarafi: Kungiyar NLC ta fadi ranar tsunduma yajin aiki, ta tura bukatu 6 ga gwamnati

Sabiu, a cikin sanarwar, ya bayyana shugaban ƙungiyar lauyoyin da ke batunci ga Kyari da manyan jami'an kamfanin, watau Adesina Bernard, a matsayin masu yin kutse ta hanyar fakewa da ƙungiya, don yin batunci ga a jagorancin Kyari da mataimakinsa Umar Ajiya.

NAM ta ce wadannan lauyoyi, tare da 'barayin' danyen man fetur din suna adawa ne da yadda Kyarin da mataimakinsa Umar Ajiya su ke bankaɗo haramtattun matatun man fetur mallakar manyan 'ɓarayin' ƙasar nan.

NAM ta kallubalanci masu neman an sauke Kyari su bayyana laifinsa cikin awa 24

Har wa yau, NAM ta kalubalanci kungiyar lauyoyin da ta fito fili ta fada wa 'yan Najeriya waye a NNPC yake da kwazo da rashin tsoro irin na Kyari da Umar Ajiya, nan da awoyi ashirin da hudu.

A karshen sanarwar, Kungiyar ta NAM ta nuna jimaminta game da yadda mutanen yankin Arewa inda Kyari ya fito, suka yi shiru kan gangamin batancin da ake masa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

Daga nan sai ƙungiyar ta gargadi lauyoyin, inda ta ce:

“Ba za mu kara naɗe hannayenmu muna kallon masu tallata ƙabilanci da 'ɓarayin' man fetur ke ɗaukar nauyinsu ba, suna yunƙurin batunci a kafafen yada labarai ga shugabancin Kyari da Umar Ajiya ba."

Daga nan sai ƙungiyar ta bayyana cewa:

“Majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa wasu tsirarun mutane a matakin gudanarwa a cikin NNPC, tare da wasu jiga-jigai da aka yi wa ritaya suke ta makirce-makirce a halin yanzu. Kuma burinsu shi ne daƙile nasarorin da shugabancin Kyari da Umar Ajiya ta samar; ba komai ba ne face ’yan baranda, mahassada, kuma ba za su yi nasara ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164