Kotu Ta Ba EFCC Umurnin Kamo Wani Hamshakin Dan Kasuwa Kan Zambar Naira Biliyan 4.8

Kotu Ta Ba EFCC Umurnin Kamo Wani Hamshakin Dan Kasuwa Kan Zambar Naira Biliyan 4.8

  • Hukumar EFCC ta samu izini daga kotu na kamo wani dan kasuwa da ta ke zarginsa da zambar naira biliyan hudu da miliyan dari takwas a Legas
  • Wanda ake zargin tare da kamfanoninsa, Mr Ibeto, ya ki bayyana gaban kotun duk da aike masa da takardar sammaci a lokuta daban daban
  • Kotun ta ce ta fahimci wanda ake karar na son mayar da kotun wajen wasa, don haka ta bayar da takardar izinin kamo dan kasuwar don yi masa hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Babbar kotun jihar Legas da ke da zama a Ikeja, a ranar Juma'a, ta bayar da umurnin kamo shugaban kamfanin 'Ibeto Energy Development', Mr Cletus Ibeto, saboda kin bayyana gaban kotun domin fuskantar tuhumar zambar naira biliyan hudu da miliyan dari takwas da ake masa.

Kara karanta wannan

‘Ba alkalai suka janyo min rashin nasara a kotu ba’, Tsohon gwamnan PDP

Mai Shari'a Ismail Ijelu ya bayar da takarar izinin kamo dan kasuwar bayan da lauyan hukumar EFCC, Rotimi Jacobs (SAN), ya gabatar da bukatar hakan, tare da sanar da kotun cewa wanda ake zargin ya ki halartar zaman kotun ne da gan-gan, duk da cewa an aike masa da takardar sammaci ba sau daya ba.

Dr. Cletus Madubugwu Ibeto
Mai Shari'a Ismail ya bayar da zinin kamo dan kasuwar saboda gaza bayyanar sa gaban kotu Hoto: Dr. Cletus Madubugwu Ibeto
Asali: Facebook

Hukumar EFCC tana tuhumar Ibeto tare da kamfanoninsa, 'Ibeto Energy Development' da 'Odoh Holdings Limited', da laifin aikata zambar naira biliyan hudu da miliyan dari takwas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta gabatar da tuhume-tuhume akalla 10 da suka shafi hada kai, damfara, yin takardun bogi da sauransu akan Ibeto, jaridar Punch ta ruwaito.

Mr Ibeto ya ki bayyana gaban kotu a kowanne zama da ta yi

An sanya ranar sauraron shari'ar zuwa 28 ga watan Satumba da kuma 5 ga wata Oktoba, 2023, amma ya gaza bayyana gaban kotun, duk da cewa lauyan da ke wakiltarsa na halartar zaman.

Kara karanta wannan

Tsohuwar jarida dake nuna farashin naira kan dala a 1978 ta bayyana a intanet, jama’a sun girgiza

A kowanne zama da kotun ta yi, lauyan sa, Dr Onyechi Ikpeazu (SAN), na sanar da kotun cewa wanda ya ke karewa ba zai samu halartar zaman ba, saboda hali na rashin lafiya. Sai dai ya sha alwashin gabatar da shi a ranar Juma'a.

Sai dai da kotun ta zauna don sauraron shari'ar a ranar Juma'a, wani lauya na daban kuma, Daniel Awosika (SAN), ya zo a matsayin wakilinsa, da cewar Ibeto ba shi da lafiya, don haka ba zai iya zuwa zaman kotun ba.

Kotu ta bayar da izini ga hukumar EFCC ta kamo dan kasuwar

Biyo bayan hakan, Jacobs ya bukaci kotu ta bayar da izinin kamo dan kasuwar, kamar yadda Channels TV ya ruwaito.

Haka zalika, Jaridar Premium Times ta ba da rahoton yadda Jacobs ya yi ikirarin cewa wanda ake karar yana cikin Lagos, wanda da tuni hukumar ta kama shi, amma kasancewar ba ta da izinin yin hakan, ya sa ba ta yi ba.

Kara karanta wannan

Saudiyya za ta tallafawa Gaza da dala miliyan 30 domin ayyukan jin kai

A hukuncin da ya yanke, Mai Shari'a Ijelu, ya ce lauyan wanda ake karar bai bayar da wata kwakkwarar jujja ta dalilin dage zaman kotun ba. Mai shari'ar ya kuma ce ba a samar da kotu don wani ya rinka juya ta kamar waina ba, sai dai don ta yanke hukunci akan kararraki.

Da wannan kotun ta bayar da izinin kamo dan kasuwar tare da dage sauraron shari'ar zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba, 2023, domin ci gaba da shari'ar.

Yar kasuwa ta sheka lahira saboda gujewa kamen EFCC

A cikin watan Yuni, 2022, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wata 'yar kasuwa da ke zaune a Legas ta rasa ranta bayan ta garkame kanta a bandaki yayin da jami'an Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa (EFCC) suka yi yunkurin kama ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.