Ango da Amarya Sun Kirga Makudan Kudaden da Suka Samu a Daren Aurensu, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Ango da Amarya Sun Kirga Makudan Kudaden da Suka Samu a Daren Aurensu, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

  • Wani bidiyo da ya yadu na wasu ma'aurata da ke kirga kudaden da suka samu a ranar aurensu ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Ma'auratan sun zauna a kan gadonsu yayin da suka tattara da kirga damin kudin a daren amarcinsu
  • Masu amfani da intanet da suka kalli bidiyon sabbin ma'auratan sun tofa albarkacin bakunansu kan kudin da kolin da suka baje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wasu sabbin ma'aurata sun garzaya dandalin soshiyal midiya don baje kolin makudan kudaden da suka samu a wajen bikin aurensu.

"Don Allah ina so na sake bikin aure," taken da aka yi wa bidiyon da ke nuna ma'auratan da ke kirga kudaden kenan.
Ango da amarya sun nuna kudin da suka samu a wajen bikinsu
Ango da Amarya Sun Kirga Makudan Kudaden da Suka Samu a Daren Aurensu, Bidiyon Ya Girgiza Intanet Hoto: @winniekay2023
Asali: TikTok

A cikin bidiyon, ma'auratan sun jeru a kan katafaren gadonsu yayin da suke tattara kudaden da yin su bandir bandir.

Kara karanta wannan

“Ni ba waliyyi bane, Najeriya ba ta da matsala”, In ji Peter Obi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabbin kudade hawa-hawa suna ta yawo a kan gadon yayin da suke kirga su. Bayan sun kammala kirgan, matar ta dauki katon bandir din kudi yayin da take wasa da shi.

Bidiyon ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon ma'aurata

RichardDiva ya ce:

"Haka yake ni da matata. Mun samu jimillar N12,486,000. Mun shafe kamar mako1 a otel don gama hada kudaden."'

Justina James audu ya ce:

"Saboda kudi kuka yi aure.
"Babu abun da wani ai fada mani."

Slamberrry ta ce:

"Kawai na yarda da mutane ne kuma suka kirga komai suka bani."

Tiwabisco ta ce:

"A daren aurena bacci muka yi don Allah sai bayan kwana 3 muka kirga kudade."

Bambi ta ce:

"Na kirga nawa nan take da kaina na dawo...bana son jin labari."

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Elohor Abayomi ta ce:

"Wannan ni da mijina ne fa mun kirga harma sai da muka yi bacci."

Farashin Naira kan dala a 1978

A wani labari na daban, mun ji cewa wata tsohuwar jarida da ke nuna yadda farashin naira kan dala yake a shekaru 45 da suka wuce ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a.

Wani mai amfani da Facebook, Obinna Aligwekwe, ya yada jaridar a dandalin na soshiyal midiya yayin da yake tsokaci game da canjin kudi a shekarar 1978.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng