Shugabannin NNPP a Arewa Maso Yamma Sun Yi Zama Kan Batun Korar Kwankwaso a Jam’iyya

Shugabannin NNPP a Arewa Maso Yamma Sun Yi Zama Kan Batun Korar Kwankwaso a Jam’iyya

  • NNPP a Arewa maso Yamma ta hango matsala, ta zauna don tattauna matsaya da kuma yadda za a warware matsaloli
  • An yabawa Abba Kabir Yusuf bisa fara cikawa Kanawa alkawuran da ya dauka a lokacin da yake yakin neman zaben 2023
  • An bayyana matsayar jiga-jigan NNPP a Arewa maso Yamma a kokarin da ake na korar Kwankwaso a jam’iyyar kayan dadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Kaduna - Shugabannin jam’iyyar NNPP na kasa reshen Arewa maso Yamma sun yi zaman kada kuri’u don bayyana matsayarsu game da zaman dan takarar shugaban kasansu na zaben 2023, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a jam’iyyar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce da kai ruwa rana kan cewa, an kori Kwankwaso daga jam’iyyar da ya yi takara.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

NNPP ta yi zama a Kaduna kan batun korar Kwankwaso
Ya ake ciki kan batun korar Kwankwaso? Ga bayani
Asali: Original

A taron da aka yi a Kaduna, wanda ya samu jagorancin jiga-jigan NNPP, ciki har da Alhaji Shehu M. Bello (Shehun Garu), an tattauna kan matsayar ‘yan Arewa maso Yamma kan dakatar da Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsu, wani sashe ne na jam’iyyar ke kokarin kawo rudu don rusa aniya mai kyau a tafiyar da aka shafe tsawon lokaci ana yi, Kwankwasiyya Reporters ta tattaro.

Sun bayyana cewa, suna goyon bayan jagoran na NNPP, kuma suna tare da shi a wannan yanayi da ake ciki.

Matsala na zuwa a NNPP

A cewar Umar Salisu, hadimin daya daga shugabannin NNPP na kasa, Alhaji Shehu M. Bello ya ce, a taron an bayyana hango rushewar jagorancin jam'iyyar duba da korar da wasu tsiraru suka yi jagoranta Kwankwaso.

Hakazalika, ya ce taron ya ba da matsayar cewa, za a hukunta masu kokarin kawo rudu da rabuwar kai a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

A wani bidiyon kai tsaye da Hon. Saifullahi Hassan ya yada a kafar Facebook, an ga lokacin da shugabannin na NNPP ke bayyana ra’ayoyi da kuma fadin matsayarsu kan batun.

Abban NNPP a Kano ya fara cika alkawari

A taron da ya samu halartar mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, an yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano bisa fara cika alkawarun da ya daukawa Kanawa.

Wadanda suka halarci tarin sun hada da mataimakin Gwamnan jihar Kano Aminu Abdulsalam Gwarzo, kwamishinoni daga jihar Kano da kuma manyan jagororin NNPP na kowacce jiha da ke Arewa maso Yamma.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana kan makomar dan takarar jam’iyyar na shugaban kasa a zaben da ya kammala a watan Faburairu.

Kalli bidiyon:

Wasu sun amince a kori Kwankwaso

A baya kun ji cewa, wasu jiga-jigan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar NNPP reshen Arewa maso Yamma sun amince da korar Rabiu Kwankwaso daga jam'iyyar.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana goyon bayansu ga matakin korar Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a inuwar NNPP daga cikin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.