Tsohuwar Jarida Dake Nuna Farashin Naira kan Dala a 1978 Ta Bayyana a Intanet, Jama’a Sun Girgiza

Tsohuwar Jarida Dake Nuna Farashin Naira kan Dala a 1978 Ta Bayyana a Intanet, Jama’a Sun Girgiza

  • Yan Najeriya sun yi martani ga wata tsohuwar jarida da ke nuna farashin dala a naira a shekarar 1978
  • Tsohuwar jaridar ta kasance hanyar sanar da mutane game da wasan karshe na wasan Tennis tare da lissafa kyaututtukan da za a samu a dala da kuma kwatankwacinsa a naira
  • Yan Najeriya da dama sun koka kan dadin da ke tattare da zamanin da, da kuma kwatanta farashin a 2023

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata tsohuwar jarida da ke nuna yadda farashin naira kan dala yake a shekaru 45 da suka wuce ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a.

Wani mai amfani da Facebook, Obinna Aligwekwe, ya yada jaridar a dandalin na soshiyal midiya yayin da yake tsokaci game da canjin kudi a shekarar 1978.

Kara karanta wannan

Hatsarin trela da adai-daita sahu ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8

Takarda da ke nuna farashin dala da naira a 1978
Tsohuwar Jarida Dake Nuna Farashin Naira da Dala a 1978 Ta Bayyana a Intanet, Jama’a Sun Girgiza Hoto: Masym Kapliuk, Facebook/Obinna Aligwekwe
Asali: Getty Images

Tsohuwar jaridar ta kasance kafar sanar da jama'a game da wasan karshe na wasan Tennis din Lagas na 1978 tsakanin Kjell Johansson da Robin Drysdale.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darajar Naira a 1978

Babbar kyautar da aka ce za a bayar a gasar ta kai dala 13,100 wanda ya yi daidai da Naira 10,200. Sabanin haka, dala 13,100 ya haura Naira miliyan 10 a shekarar 2023, kamar yadda yake a hukumance.

Yan Najeriya da dama sun koka kan faduwar darajar naira kan dala a shekarun da suka biyo baya. Legit Hausa ta rahoto cewa daga karshe data ta fadi zuwa kasa da N1,000 a kasuwar canji yayin da CBN ya dauki matakin farfado da darajar naira a kasuwanni.

Yan Najeriya sun yi martani kan farashin naira da dala a 1978

Kara karanta wannan

'Ina da tabbaci: CBN ya dauki mataki daya tak da zai inganta naira, za ta dawo kasa da dubu 1

Nkiruka Rosemary Onwueme ta ce:

"Mahaifina ya kasance da kungiyar Tennis na LAGAS a shekarun tamanin da casa'in. Su kan buka wasa a Ebute Meta."

Kingsley Aneke ya ce:

"Sannan Dunlop ya bar kasar bayan gagarumin asara da ya yi saboda rashin saukin yin kasuwanci da matsalar wuta."

Paulinus Ugwuja ta ce:

"A kasashen da suka waye, abubuwa na kara inganta ne lokaci zuwa lokaci, amma akasin haka ne a Najeriya.
"Yanzu muna ji ina ma ace da zai dawo."

Ifeanyi Onwurah ya ce:

"1978 kafin a gina Legas....
"Hakika an yi wata kasa."

CBN ya dauki matakin inganta Naira

A wani labarin, mun ji cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya sanar da biyan bashin kudade na wasu bankuna da kamfanoni.

Rahoton bankin na 2022 kan basukan Najeriya ya tabbatar da cewa wasu bakunan kasashen waje na bin kasar makudan kudade, Legit ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng