Mawaki Lilin Baba Ya Ziyarci Gumi, Ya Bada N500,000 Tallafi Ga Yan Falasdinu

Mawaki Lilin Baba Ya Ziyarci Gumi, Ya Bada N500,000 Tallafi Ga Yan Falasdinu

  • Fitaccen mawaki Lilin Baba ya yi tattaki har zuwa wajen Sheikh Ahmad Gumi don mika taimakonsa ga yan Gaza
  • Mawaki Shu'aibu Ahmed Abbas ya mikawa Shehin malamin N500,000 a matsayin gudunmawarsa ga mutanen Falasdinu
  • Al'ummar Gaza dai suna cikin yanayi na yaki sakamakon zaluncin Isra’ila

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shahararren mawaki kuma jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Shu'aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba ya ziyarci shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.

Lilin Baba ya ziyarci Sheikh Gumi ne domin bayar da gudunmawarsa ga al’ummar Falasdinawa wadanda ke fama da yaki.

Lilin Baba ya bayar da gudunmawar kudi ga yan Gaza
Mawaki Lilin Baba Ya Ziyarci Gumi, Ya Bada N500,000 Tallafi Ga Yan Falasdinu Hoto: @Hausafilmsnews
Asali: Twitter

Mawakin ya ba shehin malamin N500,000 domin a saka a cikin asusun banki wanda za a tura don taimakawa mutanen Falasdinu yayin su ke cikin wani yanayi na zalunci daga Isra’ila.

Kara karanta wannan

Kabilanci, Kudi da Abubuwa 10 da Za Su Yi Tasiri a Zaben Kogi Nan da Kwanaki 6

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani kira Gumi ya yi wa Musulmai kan yan Falasdinu?

Tun a ranar Juma’a, 20 ga watan Oktoba ne Gumi ya sanar da bude asusun taimakon a cikin wani faifan bidiyo yayin wani karatunsa inda ya jaddada wajibcin yin hakan.

Ya shawarci sauran malamai da su hada kai don ganin sun gayyaci wakilin Falasdin da ke ofishin jakadancinsu a Abuja don ba su wannan taimako.

Ya ce taimako ba wani abu ba ne inda ya kiraye Musulmi a kan kowa ya kawo taimakonsa yana mai cewa Yahudawa ba abin amincewa ba ne.

Shafin da ke kawo labaran da suka danganci masana’antar Kannywood mai suna @Hausafilmsnews ne ya sanar da ci gaban a Twitter inda ya ce:

“Masha Allah… Mawaki Kuma Jarumi @lilinbaba_ ya ziyarci Sheikh Gumi inda yabada gudun muwarsa ga alummar falasdinawa #500,000 Allah yasakamai da alkhairi.”

Kara karanta wannan

Majalisar sarakunan Arewa sun goyi bayan Sarkin Hausawa da aka dakatar kan raina Olubadan na Ibadan

Jama’a sun yi martani yayin da Lilin Baba ya ba da gudunmawar kudi ga yan Falasdinu

@Saleibr44624203 ya yi martani:

"Masha Allah fatan alkairi."

@Duwan3pointO ya yi martani:

"Wannan askin nakan lilin Baba Haram ne... Annabi ya Hana.. wani ya fada masa..."

@Hussein88603522 ya yi tambaya:

"Toh shi gumi ake kaiwa kuɗin?"

@ShuaibSabit ya ce:

"Ameen Allah yasaka mashi da alkhairi."

@AbdullahiM63883 ya ce:

"Masha Allah."

@masudal50880564 ya ce:

"Masha Allah"

Legit Hausa ta turawa mawakin sako ta shafinsa na sadarwa don jin karin bayani daga wajensa amma bai amsa ba tukuna.

Bolivia ta dauki mataki kan Isra'ila

A wani labarin, mun ji cewa kasar Bolivia ta zamo kasar Nahiyar Amurka daya tilo da ta yanke alaka da Isra’la saboda hare-haren ta’addanci kan Gaza.

Gwamnatin Bolivia ta kirayi tsagaita wuta tare da bukatar bude kofofin kai agaji yankin Gaza da ke shan hare-hare, cewar Reuters.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng