Kano: Kotun Tarayya Ta Yi Hukunci Kan Matakin Abba Kabir Yusuf Kan Makarantu Ma Su Zaman Kansu
- Kotu ta dakatar da Gwamna Abba Kabir na daukar mataki kan makarantu ma su zaman kansu a jihar
- Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ita ta ba da wannan umarni ga gwamnatin jihar
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya soke lasisin dukkan makarantu ma su zaman kansu a jihar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Babbar kotun Tarayya a jihar Kano ta dakatar Gwamna Abba Kabir na jihar Kano na daukar mataki kan makarantu ma su zaman kansu.
Mai Shari’a, Nasiru Saminu shi ya ba da wannan umarni bayan shigar da kara da Barista AbduHafees Khalid ya yi.
Mene gwamnatin Kano ta yi?
Gwamnatin Kano a watan Agusta ta soke lasisin gaba daya makarantu ma su zaman kansu a jihar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda ake karar akwai gwamnatin jihar Kano da Gwamna Abba Kabir da kwamishinan shari’an jihar.
Sauran sun hada da hukumar kula da makarantu ma su zaman kansu a jihar da kuma Kwamred Baba Abubukar Umar.
Wane mataki kotun ta dauka?
Har ila yau, wadanda su ka shigar da kara sun hada da Kungiyar makarantu ma su zaman kansu ta kasa da kuma ta jihar da kungiyar ma su makarantun Islamiyya.
Kotun ta umarci shugabanni da ma’aikata da sauran ma su ruwa da tsaki a cikin wadanda ake karar da su janye kudurinsu, SolaceBase ta tattaro.
Ta kara da cewa dole su jira har sai lokacin da aka kammala wannan shari’a don sanin matakin da za su dauka a gaba.
Mai Shari’a Saminu ya dage ci gaba da sauraran shari’ar har sai ranar 21 ga watan Nuwamba na wannan shekara.
Abba Kabir ya soke lasisin makarantu ma su zaman kansu
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir ya soke lasisin makarantu ma su zaman kansu gaba daya a jihar Kano.
Baba Abubukar, mai bai wa gwamnan shawara kan makarantun shi ya bayyana haka a ranar 12 ga watan Agusta a Kano.
Baba ya kara da cewa ana sa ran gaba daya makarantun za su sake yin rijista tare da bin dukkan ka’idoji.
Asali: Legit.ng