Masallacin Abuja: Wike Ya Wanke Kansa, Ya Ba da Gagarumar Gudunmawa Don Inganta Masallaci

Masallacin Abuja: Wike Ya Wanke Kansa, Ya Ba da Gagarumar Gudunmawa Don Inganta Masallaci

  • Minista Nyesom Wike na Abuja ya amince da fitar da wasu kudade don gyara da kula da masallacin Abuja
  • Har ila yau, Wike ba da makudan kudade don gyara cibiyar Kiristoci da ke birnin Tarayya Abuja
  • Wike ya bayyana jin dadinsa ganin yadda ayyukan ke tafiya ba tare da matsala ba duk da tasgaro da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike ya amince da ba da makudan kudade don kula da masallacin Abuja da cibiyar Kiristoci.

Wike ya bayyana haka a jiya Alhamis 2 ga watan Nuwamba yayin ran gadi zuwa wuraren ibadar na Musulmi da Kiristoci a Abuja.

Wike ya amince da makudan kudade don gyaran masallacin Abuja da cibiyar Kiristoci
Minista Wike ya ba da gudunmawa ga masallcin Abuja. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Mene Wike ya bayar a masallacin Abuja?

Kara karanta wannan

Wike Ya Zauna da ‘Yan Majalisa, Ya Jaddada Sharudan Sasantawa da Gwamnan Ribas

Ministan ya ce ya ji dadin yadda aka yi aiki a ingantacce a wuraren ibadar duk da tasgaro da aka samu a farko daga ‘yan kwangila, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce cibiyar Kiristocin ta bukaci kudade don karasa gyara kashi na biyu inda ya ce idan hukumar FCT ba ta da kudaden zai yi magana da Shugaba Tinubu.

Ya ce:

“An amince da ci gaba da gyaran masallacin Abuja da kuma cibiyar Kiristoci bayan an tsayar da aikin saboda karin wasu ayyuka da ya kamata a yi.
“Na ji dadin yadda aiki ke tafiya a nan kuma na amince da ba da makudan kudade ga ‘yan kwangila don karasa wannan aiki mai muhimmanci.”

Wane tabbaci Wike ya bayar kan addinan biyu?

Ya kara da cewa wannan ayyuka da za a yi a wuraren ibadar addinan guda biyu na daga cikin himmatuwar Tinubu na inganta rayuwar al’ummar kasar.

Kara karanta wannan

Saudiyya za ta tallafawa Gaza da dala miliyan 30 domin ayyukan jin kai

Har ila yau, Wike ya tabbatar da cewa Tinubu na tare da dukkan addinan guda biyu saboda samar da ingantaccen shugabanci a kasar, cewar TheCable.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin ministan da shirya rushe wani bangare na masallacin Abuja a kokarin fadada wata hanya da ta biyo wurin.

Wike ya yi martani kan zargin kin Musulunci

A wani labarin, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi martani kan zargin da ake ma sa cewa ya na kin addinin Musulunci.

Wike ya tabbatar da cewa ba shi da wannan akida a zuciyarshi inda ya ce babu wanda ya ke mutuntawa kamar Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.