Babbar Kotu Ta Yanke Hukuncin Kan Ƙarar Tsohon Gwamnan Babban Banki CBN Emefiele

Babbar Kotu Ta Yanke Hukuncin Kan Ƙarar Tsohon Gwamnan Babban Banki CBN Emefiele

  • Wata Kotu a babban birnin tarayya Abuja ta bada umarnin gaggauta sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele
  • Ta ce a sake shi ba tare da gindaya masa wasu sharuɗɗa ba, inda ta umarci EFCC da shugaban hukumar su aiwatar da wannan umarni
  • Wannan ya biyo bayan rokon da Emefiele ya yi wa Kotun domin a ba shi dama ya shaƙi iskar ƴanci kamar kowane ɗan kasa

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babbar Kotun birnin tarayya Abuja ta ba da umarnin a gaggauta sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Kotun ta bada umarnin sakin Emefiele ba tare da gindaya masa wani sharaɗi ba kuma cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

A Ƙarshe, Gwamnan APC ya tona gaskiyar abinda ya sa Shugaban NLC na ƙasa ya ci dukan tsiya a Imo

Tsohon gwamnan CBN a Kotu.
Babbar Kotu Ta Yanke Hukuncin Kan Ƙarar Tsohon Gwamnan Babban Banki CBN Emefiele Hoto: Godwin Emefiele
Asali: Twitter

Kotun ta bada wannna umarni ne bayan Emefiele ya shigar da buƙata, inda ya nemi a sake shi ya shaƙi iskar ƴanci daga wurin da yake tsare a hannun hukumar EFCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Don haka tsohon gwamnan babban bankin ya roƙi Kotu ta bada umarnin a sake shi ya koma gida gabanin yanke hukuncin ƙarshe a shari'ar.

Wane hukunci Kotu ta yanke kan buƙatar?

Da yake yanke hukunci, Mai shari'a O.A. Adeniyi, shi ne ga bada wannan umarni na sakin tsohon gwamnan CBN ɗin bayan sauraron koken Emefiele.

Mai ƙara watau Emefiele ya ambaci gwamnatin tarayyan Najeriya, Antoni Janar na ƙasa, shugaban EFCC da ita kanta hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a matsayin waɗanda yake ƙara.

Umarnin da Kotu ta bayar kan Emefiele

Umarnin Kotun ya ƙunshi muhimman abubuwa da suka haɗa da, gaggauta sakinsa ba tare da sharaɗi ba da umarnin shugaban EFCC da hukumar su sake shi nan take.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da CoS na shugaban majalisar dokokin Adamawa, sun turo saƙo mai tada hankali

Ko kuma Kotun ta ba su zaɓin zasu iya bari su gurfanar da shi a gaban Kotu a zama na gaba, wanda mai yiwuwa a bada belin Emefiele a wannan rana.

Daga nan Kotun ta ɗage zaman zuwa ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023 da misalin ƙarfe 1:00 na rana domin sauraron wasu korafe-ƙorafe, Daily Post ta ruwaito.

Sanatoci 2 a Borno sun san makomarsu a Kotu

A wani rahoton na daban Kotun ɗaukaka ƙara ta raba gaddama kan sahihancin zaɓen Sanatocin jam'iyyar APC biyu daga jihar Borno.

A zaman yanke hukunci, kwamitin alƙalan Kotun ya kori karar da aka ƙalubalanci Ali Ndume da Kaka Lawal bisa rashin cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262