Ina da Tabbaci: CBN Ya Dauki Mataki Daya Tak da Zai Inganta Naira, Za Ta Dawo Kasa da Dubu 1

Ina da Tabbaci: CBN Ya Dauki Mataki Daya Tak da Zai Inganta Naira, Za Ta Dawo Kasa da Dubu 1

  • Babban bankin CBN ya dauko matakin da zai farfado da darajar naira a kasuwanni da kuma na bayan fage da ake hada-hadar naira
  • Bankin ya ce ya dauki matakin ne don tabbatar da kawo daidaito a yanayin yadda darajarta ke kara zubewa
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin Bola Tinubu ta himmatu wurin tabbatar da farfado da darajar naira a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Babban Bankin Najeriya, CBN ya sanar da biyan bashin kudade na wasu bankuna da kamfanoni.

Rahoton bankin na 2022 kan basukan Najeriya ya tabbatar da cewa wasu bakunan kasashen waje na bin kasar makudan kudade, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tsohuwar jarida dake nuna farashin naira kan dala a 1978 ta bayyana a intanet, jama’a sun girgiza

CBN ya dauki matakin daga darajar naira a Najeriya
Bankin CBN ya dauki matakan daga darajar naira a kasuwanni. Hoto: CBN.
Asali: UGC

Nawa yawan basukan da CBN ya ce ake bin Najeriya?

Bankunan kasashen waje kamar su JP Morgan da Goldman Sachs na bin Najeriya kudin da ya kai dala biliyan 13.8.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan akwai wasu karin basukan da su ka kai naira biliyan 3.15 da su ke bukatar a biya su don inganta zuba hannayen jari daga kasashen waje.

BusinessDay ta tattaro cewa bankin CBN ya fara biyan kudaden inda ya biya kusan kaso 75 zuwa 80 na basukan.

Bankunan da aka biya kudaden sun hada da bankin Citi da Standard da kuma bankin Stanbic IBTC.

Wane amfani matakin CBN ke da shi kan naira?

Wannan mataki na CBN na biyan basukan zai kara farfado da darajar naira a duniya a kasuwannin hukumomi da kuma na bayan fage.

Ana sa ran idan aka kammala biyan basukan hakan zai kara daga darajar naira a kasuwannin tare da rage yawan nemanta a kasuwannin bayan fage.

Kara karanta wannan

Hobbasan sabon Gwamnan bankin CBN ya yi sanadiyyar zaburar darajar Naira

Har ila yau, idan hakan ta faru, zai farfado da darajar naira wanda ake sa ran farashin zai gaza naira duba daya.

CBN ya ba da dala biliyan 5 don inganta naira

A wani labarin, Babban Bankin Najeriya, CBN ya zuba dala biliyan biyar don farfado da darajar naira a kasuwanni a kasar.

Wannan matakin na CBN an dauke shi ne don kare naira daga durkushewa a kasuwanni kamar yadda kullum ta ke zubewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.