Saudiyya Za Ta Tallafawa Gaza da $13M Domin Ayyukan Jin Kai
- Sarki Salman da yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman, za su fitar da dala miliyan 13 domin kai dauki ga al'ummar da yaki ya rutsa da su a Gaza
- Tallafin zai zo daga aljihun sarkin da yarima, amma za a bayar da shi ne karkashin cibiyar ayyukan jin kai da agajin gaggawa ta Sarki Salman (KSRelief)
- UN ta ajiye kokon bararta ga duk wanda ya ke da hali domin tara akalla dala miliyan 300, wanda za ta yi amfani da kudin don kai agajin gaggawa a Gaza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Saudiyya - Kasar Saudiyya za ta sake ware wata dala miliyan 13 domin gudanar da ayyukan agaji a Gaza, kamar yadda cibiyar ayyukan jin kai da agajin gaggawa ta Sarki Salman (KSRelief), ta sanar a ranar Alhamis.
Sarki Salman da yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ne za su bayar da kudin daga aljihunan su, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito
KSRelief, da aka samar da ita a shekarar 2015, na aiki tare da kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana bayar da tallafin jin kai ga kasashe sama da 100.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan da yaki ya barke tsakanin kasar Isra'ila da Hamas, ofishin bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya aike da kokon barar neman tallafin akalla dala miliyan 300 ga duk wanda ke da halin taimaka wa.
Halin da jama'ar Gaza suke ciki
Al'ummar Gaza na ci gaba da samun tallafi daga kungiyoyi da kasashe da dama tun bayan da fada ya kaure tsakanin mayakan kasar Isra'ila da Hamas, bayan harin da aka fara a ranar 7 ga watan Oktoba.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa sama da 'yan kasashen waje 7,000 ne ke kokarin ficewa daga yankin ta iyakar Rafah a Egypt.
Ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza ya ce hare haren sama da kasar Isra'ila ke kai masu, na dita kai tsaye ga sansanonin gudun hijira, kuma tana yin hakan ne da gangan.
Jaridar Aljazeera ta ruwaito cewa hare haren da Isra'ila ta kai Gaza sun ruguza gine ginen mutane a sansanin Jabalia, al-Shati, al-Bureij da al-Maghazi, a cewar ofishin watsa labaran.
Tun bayan fara kai hare hare ba tare da tsagaita wuta a Gaza ba, Isra'ila ta jefa akalla tan 250,000 na abubuwan fashewa a yankin.
Babu Abinci, Babu Lantarki, Isra'ila Ta Toshewa Falasdinawa Hanyar Rayuwa
Ministan tsaron Israila, Yoav Gallant ya bada umarnin a toshe hanyar ruwa a Gaza ta yadda Falastina ba za ta samu wutar lantarki ko abinci ba.
Times Of Israel ta rahoto cewa dakarun kasar Israila za su rufe hanyar da kayan abinci, fetur ko lantarki zai su iya kai wa ga 'yan Gaza.
Asali: Legit.ng